Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Masarautar Jaba

Rahotannin da muke samun a halin yanzu daga Jihar Kaduna na cewa yan bindiga sun sace wani Sarki mai daraja ta daya Sarkin Masarautar Jaba Kpop Ham, Dokta Jonathan Danladi Gyet Maude (JP, OON) wanda sanannen Sarki ne kuma jagoran al’ummar Jaba cikin Jihar Kaduna.

Rahotannin da muke samu na bayanin cewa an sace shi ne a Gonarsa da ke Jihar Nasarawa.

Rundunar tsaro ta Yan Sanda a Jihar Kaduna na cewa su na nan su na tuntubar abokan aikinsu daga Jihar Nasarawa, domin sanin ko yaushe lamarin ya faru.

Jihar Kaduna dai na cigaba da fuskantar barazanar ‘yan Bindiga, musanman akan manyan sarakuna, inda a kwanakin baya ma ‘yan Bindigar suka sace mai Martaba Sarkin Kajuru.

Related posts

Leave a Comment