An kama Mutane biyar a Kano da suka yiwa wani Dan Shekara 20 fyade a Jahar Kano
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da Mai Magana da Yawun Rundunar Yansandan Jahar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a Kano.
Yansandan sunce wata mata dake zama a unguwar Mandawari dake Kano, ta kawo rahoton a ofishin Yansanda.
Yansanda sunce wadanda aka kama sun hada da Ahmed Inuwa Dan Shekaru 34, da Nasiru Isyaku Dan Shekaru 48, da Lawan Uba Dan Shekaru 31 da Kuma Auwal Uba Dan Shekaru 40 gami da Rabiu Sharu Dan Shekaru 33.
An dai yi gaggawar kai Wanda Lamarin ya faru dashi Asibitin Koyarwa na Muhammadu Abdullahi, Kano, inda akayi mashi magani, aka Kuma sallame shi, inji shi.
Haruna Kiyawa yace, Kwamishinan Yansandan Jahar CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umarci tawagar Yansanda data kamo wadanda suka aikata laifin.
“Tawagar sunyi gaggawar bin umarnin, inda suka kamo dukkanin masu laifin guda 5 Wanda aka ambata da laifin. Haka Zalika, a lokacin da aka bincike su, sun tabbatar da aikata laifin”, Inji shi.
Haruna Kiyawa ya kara dacewa, ana yin bincike, kuma da an kammala za’a mika su Kotu domin zartar masu da hukunci.
