Rahotanni daga ?asar Amurka na bayyana cewar wani Banki dake kasar ya rufe asusun ajiyar ?ungiyar Tsagerun Inyamurai ta IPOB ?arkashin jagorancin Nnamdi Kanu dake garkame a Najeriya.
A cewar rahoton Sanarwar da Chika Edoziem, shugaba a kungiyar ta IPOB, ya fitar a ranar Alhamis ta ce ana amfani da asusun ajiyar ne domin karbar kudaden da mambobin IPOB ke biya duk wata.
Edoziem ya ce an rufe asusun ajiyar ne biyo bayan samun rahoto daga bankin na cewa wasu mutane da ba a bayyana ko su wanene ba suka zargin ana aikata zamba da asusun ajiyar wajen wasu aikata wasu laifuka.
Ya ce an bude wani sabon asusun ajiyar banki da mambobin za su cigaba da biyan kudadensu na wata, yana mai shawartarsu da su yi biyaya ga sabon umurnin.
“Shugaban kungiyar IPOB na duniya baki daya, Nnamdi Kanu, ya bada umurnin bude sabon asusun ajiyar banki na IPOB a Amurka, ana umurtar mambobi su cigaba da biya kudadensu na wata.
“Wannan asusun na Amurka shine asusun da shugaban mu ya ce a rika tura kudin tallafi na ESN. “Sakamakon rahoton da wasu da ba a san ko su wanene ba suka tura wa bankin na alakanta asusun da zamba, banki ta bukaci a rufe asusun.”
