Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun yi nasarar sake kubutar da yara ashirin da takwas daga cikin yaran da aka sace a makarantar Bethel Baptist High Secondary School ta Jihar Kaduna.
An yi nasarar kubutar da su ne yau Lahadi, inda tuni iyayensu suka karbe su a harabar makarantar.
A watan da ya gabata ne wasu gungun ‘yan Bindiga suka dira Makarantar ta Bethel Baptist, inda suka yi awon gaba da dalibai kimanin 200 cikin dokar daji.
Jihar Kaduna dai na fuskantar barazanar ‘yan Bindiga matuka, tun bayan kurarin da gwamnan Jihar El Rufa’i ya yi na cewar ba zai yi sulhu da ‘yan Bindiga ba.
