Pantami Ya Wakilci Nijeriya A Taron Kamfanin Wayoyin Zamani Na Duniya

Ministan Sadarwa da raya Tattalin Arziki na Tarayyar Nijeriya Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci tawagar Nijeriya daga bangarorin gwamnati da na masu zaman kansu a taron “Mobile World Congress (MWC)” da ke gudana a garin Barcelona, dake kasar ??Spain.

Kamfanin MWC babbar masana’antar samar da manyan wayoyi ce ta hannu da samar da abubuwan sabbin fasahohin zamani.

Taron ya samu halartar masu wayoyin hannu na duniya, masana’antun na’urori, masu samar da fasaha, masu siyarwa, masu hannun jari, da sauransu.

Duk a cikin kokarin Minista Pantami, na ganin kasar Nijeriya ta kera manyan wayoyin zamani masu arha ga ‘yan kasar.

Related posts

Leave a Comment