Kamfanin Mai na ?asa NNPC ya jaddada aniyarsa ta cigaba da inganta rayuwar al’ummar Najeriya da ababen more rayuwa da taimakawa wajen samar abin yi ga Matasa.
Shugaban Kamfanin NNPC Malam Mele Kyari ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tattauna albarkatun Mai da iskar Gas na shekarar 2021 wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.
Mele Kyari ya kara da cewar Najeriya a matsayin ?asa mai yawan matasa ya zama dole ayi duba da samar da hanyoyin inganta rayuwar matasa a matsayin su na kashin bayan cigaba na kowace al’umma.
Ya kara da cewar tuni kamfanin ya kammala aiki na biyu na bututun mai na Legas domin fadada ayyukan samar da mai da iskar gas, wanda aikin zai hade da na Ajaokuta-Kaduna zuwa Kano yayin da aikin Obiafu-Obrikom ya ke dab da kammala a kwanan nan.
Kyari ya kara da cewar babban burin kamfanin shine yadda zai wadata ‘yan Najeriya da ha?aka arzikin su ta fuskar ayyukan yi da kasuwanni.
Kamfanin na NNPC na da burin kar?ar kashi 20 na hannun jarin Matatar mai ta ?angote domin ?ara ha?aka ayyukan samar da Mai a fadin ?asa.
“Akwai hanyoyin da kamfanin na NNPC ke bi wajen ganin jama’ar Najeriya sun amfana tare da cin gajiyar albarkatun ?asa ta hanyar hadin gwiwa da kasuwanci wanda zai ciyar da kasa gaba”.
Mele Kyari ya kuma bayyana batun dokar Mai da Majalisar ?asa ta amince dashi da cewar zai taimaka matuka wajen kai wa ga bukatar da ake da ita na habaka kasuwanci da arzikin ‘yan ?asa.
