Babu Hujja A Bidiyon Karbar Dalolin Ganduje – Hukumar Yaki Da Rashawa


Shugaban Hukumar Hana Rashawa na Jihar Kano, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa akwai dalilan da su ka nuna zai yi wahala a lokacin da aka nuno bidiyon da aka ce Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ri?a cusa damman daloli a cikin aljifai a ce an bincike shi.

Jaridar Daily Nigerian ce ta ri?a wallafa bidiyon ?aya bayan ?aya, wanda nan da nan ya zubar wa Ganduje mutunci a ?asa warwas.

A ranar 12 Ga Yuni, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa an rasa wanda zai fito ya yi aikin tare da masu binciken da za su gurfanar da gwamnan.

Ya ce bidiyon farko da aka fara nunawa, an ri?a jin sautin da aka ?ora kan bidiyon daga baya, kuma an yi masa fassara da Turanci.

” Bayan wani da bai bayyana kan sa ya aiko wa ofishi na da wasi?ar kiran a yi bincike, mun sanar da manema labarai cewa akwai hanyar yin bincike ko da kuwa mai ?orafi ba ya son bayyana a gaban kwamiti.”

Ya ce an ri?a neman hukumar ta yi bincike, amma yayin da aka ri?a bin lambar wayoyin su da adireshin da su ka bayar, sai aka gano duk adireshin na bogi ne.

“Sannan kuma mu ka gayyace su domin su bayyana a gaban kwamiti, amma duk su no?e babu wanda ya bayyana. Ka ga sun yanke hujja kenan. Kuma babu wata hukumar da za ta iya binciken wannan lamari a haka, har a ce an gurfanar da gwamnan.” Inji Magaji.

Magaji ya ?ara da cewa kafin mai gabatar da ?ara ya gurfanar da wanda ake zargi, tilas sai ya samu ?wararan hujjoji tukunna.

Ya ce a lamari irin wannan akwai bu?atar ha?in kai daga wasu hukumomin da?ile rashawa domin su bayar da shawarwari na ?warai.

Bayan maganar ta tu?e a majalisa ne dai Ganduje ya maka Ja’afar Ja’afar kotu, inda ya ce an shirya bidiyon ne don a ta?iye shi kada ya ci za?en 2019.

Batun ya sake tashi watannin baya, inda Ja’afar ya ce ana yi masa barazana ga rayuwar sa. Daga nan ya tsere Ingila.

Related posts

Leave a Comment