Shugaban EFCC, wato hukumar dake ya?i da cin hanci da kar?ar rashawa na ?asa wato Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa ana yawan yi masa barazan da rayuwar shi tun bayan da aka bashi shugabancin hukumar ta EFCC.
Bawa yace lallai mutanen da suke ya?a bisa laifukan cin hanci suma suna maido da martani ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Buhari ma ya ta?a yin irin wannan furuci a shekarar 2016.
Shugaban EFCC yayi wannan jawabi ne yau talata a wata hira da aka yi shi a wani shiri na gidan talabijin ?in Channels Tv.
Da aka tambaye shi ko yakan fuskanci barazana a yayin gudanar da ayyukan shi, sai ya kada baki yace: “Idan zaku iya tunawa naje birnin New York a satin da ya gabata. Wani babban mutum yake ce mun ya kar?i kiran waya daga wani mutum wanda binciken EFCC bai ma biyo ta kanshi ba, inda yake mishi i?rarin cewa shi sai ya kashe shugaban EFCC wannan matashin yaron. Kamar yadda The Eagle ta wallafa.
“Ya jaddada mishi cewa ‘zan kashe shi, sai na kashe shi.’ wannan ne zai gwada maka yadda masu cin hanci ke nasu iya ?o?arin wajen gani bayanmu.”
Da aka tambaye shi kan cewa ko an ta?a mishi barazanar mutuwa, sai ya kada baki yace ‘eh, an ta?a mishi.’
A watan Fabrairun wannan shekarar ne dai shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya na?a Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC biyo bayan turka-turkar data janyo cire tsohon shugaban hukumar wato Ibrahim Magu.
Source: The Eagle Online
