Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karya darajar naira a hukumance sakamakon fara aiki da ya yi da sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX).
CBN ya rage darajar ku?in da kashi 8 cikin 100, inda yanzu take N410.25 kan kowace dala ?aya.
Kazalika bankin ya bayyana sauyin ?arara a shafinsa.
Mako biyu da suka wuce kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa bankin zai karya darajar naira ta hanyar sauka daga kan N379 kan kowace dala ?aya domin tsayar da farashin nairar guda ?aya a kasuwa.
Wannan sauyin na nufin daga yanzu kasuwa ce za ta dinga fayyace darajar naira ko kuma farashinta yayin canji.
Najeriya ta da?e tana amfani da tsaruka mabambanta wajen canjin ku?a?en ?asar waje, abin da ya sa CBN ya mayar da hankali kan tsari guda ?aya kenan a yanzu.
Babu tabbas game da yadda darajarta za ta kasance a kasuwar bayan fage, yayin da a ‘yan kwanakin nan nairar ke kaiwa har kusan N490 kan dala ?aya.
Yadda ake canzar da dala da yuro da fan a farashin gwamnati:
- Dala – $1/N410.25
- Fan – £1/N579.64
- Yuro – €1/N501.07
