Badakalar Biliyan 166: Majalisa Ta Yi Sammacin Hadiza Da Ministan Sufuri

Majalisar Wakilai ta tarayya a ranar Alhamis ta aike da takardar sammaci ga ministan sufuri Rotimi Amaechi da hukumar gudanarwa ta tashoshin jiragen ruwa dangane da ?atan dabo na wasu ma?udan ku?a?e da hukumar ta tara na haraji a shekarar 2016 da suka haura sama da naira Biliyan 166.

Majalisar ta gano cewar wadannan ma?udan ku?a?e ba’a sanya su cikin lissafin kudaden da suka shiga asusun hukumar ma da sauran aikace-aikacen ta.

Shugaban Kwamitin dake kula da asusun tarayya na majalisar Busayo Oluwole Oke ya fitar da takardar sammacin bayan kin halartar da ministan da hukumar tashoshin jiragen ruwa da jiragen ?asa gaban kwamitin bincike na ofishin Akanta Janar na tarayya.

Bisa ga haka ne Shugaban kwamitin na majalisar ya bayyana cewar sun bayar da ranar 8 ga watan Yuli ga Ministan da Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa da su bayyana gaban majalisa domin bayani.

Ya ?ara da cewar dukkanin bangarorin biyu na Minista da hukumar tashoshin jiragen ruwa zasu yi bayani akan wasu kudade da suka kai Naira biliyan 103.996 na ayyukan da hukumar tace tayi da ?arin wasu kudade na naira Biliyan 65.130 da Naira biliyan 38.412 na wasu ayyukan hukumar.

“An sa ran bangarorin biyu zasu warware zare da abawa akan batun wanda Akanta Janar ya fitar tun a shekarar 2016 amma shiru har zuwa yau”.

Ya ?ara da cewar ana sa ran ministan da hukumomin tashoshin jiragen zasu fayyace yadda suka sarrafa ku?a?en shiga na Hukumar da ayyukan da aka yi dasu a lokacin da suka bayyana gaban Kwamitin Majalisar.

Related posts

Leave a Comment