Najeriya Za Ta Cigaba Ne Kawai Idan An Cire Tallafin Mai – Ministan Mai

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya sake nanata bukatar sake fasalta sashen man fetur ta hanyar sanya farashin kayayyaki kamar yadda kasuwa ke bi don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Mista Sylva ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a taron Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja.

Da yake bayyana dalilansa na cewa dole a cire tallafin, ministan cewa ya yi: “Zan iya cewa matsaya ta a kan tallafin mai da sake fasali sanannu ne. Na yi imanin cewa domin wannar kasa ta ci gaba, domin tattalin arzikinmu ya samu ci gaban da ake so, muna bukatar tsayar da farashin kayayyakin mai kamar yadda suke a kasuwa.

“Lokacin da kuka samar da wani abu a wani akan farashi mai tsada kuma kuka sayar da shi a farashi mai sauki ga mutane saboda kuna dauke wa mutane wasu nauyin da ke kansu ba shi ne mafi kyau ba.

“Abu ne da ake matukar so, amma kuma ba mai dorewa ba ne saboda abin da ke faruwa shi ne ku samar da abu a N10, ku sayar da shi N5; gobe, ku sake nemo shi a N10, ku kara N5 daga wani wuri, ku sake samar da shi a N10 ku siyar da shi kan N5.

“Don haka, asarar tana karuwa kuma tana hauhawa a kowace rana kuma wannan asarar da ake yi ita ta kawo mu inda muke.”

Related posts

Leave a Comment