Najeriya Za Ta Kasance Jagaba A Afirka Ta Fuskar Fasahar Zamani – Pantami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzi?in zamani, Dr. Isa Pantami yace Najeriya ta kai wani matsayi a yanzu ta fuskar fasahar zamani a jerin kasashen duniya, kuma tana da damar da zata samar da layukan waya da manyan wayoyin hannu ga ?asashen Africa.

Ministan ya fa?i haka ne a wani taro da jam’iyyar APC ta shirya ranar Alhamis a Sakateriyar jam’iyyar dake Abuja. APC ta shirya taron ne ga hadiman gwamnati su baje kolin nasarorin da suka samu tun sanda suka shiga ofis ga ‘yan Najeriya.

Yayin da Pantami ke jawabi a wajen taron, ya tabbatar da cewa daga yanzun za’a daina shigo da layukan waya daga ?asashen waje da sauran kayan sadarwa saboda kashi 60-70% Najeriya zata rin?a samar da su, ga ‘yan kasa har da kasashen waje.

A cewar ministan Najeriya tana da ?arfin da zata iya samar da layukan waya 200 miliyan duk shekara, cikin natsuwa da kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Pantami yace: “Munzo da sabon tsari wanda nan da shekara 2 zuwa 3, mafi karanci kashi 60-70% na abinda muke bu?ata ta ?angaren sadarwa zamu samar dashi a cikin gida Najeriya.”

“Lokacin da wannan gwamnatin tazo, layukan waya bama iya yi sai an kawo mana daga waje. Amma yanzun gwamnatin tarayya ta baiwa masu zaman kansu damar su samar da layukan waya, ba wai ga ?asa ka?ai ba harda kasashen Africa.”

“Muna da ?arfin da zamu iya samar da layukan waya miliyan 200 a shekara. Yanzu a Najeriya muna samar da manyan wayoyin hannu.”

Related posts

Leave a Comment