Talakawa Miliyan Guda Za Su Ci Moriyar Dubu Biyar-Biyar A Watanni Shida – Sadiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan ?aya da matsalar cutar korona ta shafa za su ri?a kar?ar Naira 5,000 a kowane wata har tsawon watanni shida.

Ta ce wannan ya na cikin wani sabon shiri ne da ya fara aiki a farkon wannan shekarar da mutum 3,115 a Legas da Abuja, wanda yanzu za a fa?a?a shi zuwa sauran dukkan jihohi inda mutane za su fara amfana da shi su ma.

Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka yi ran Talata a Abuja inda ta yi ?arin bayani kan shirin nan na rage ra?a?in fatara da yunwa a ?asar nan, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP).

A cewar ta, an bu?e rajistar kawo ?aukin gaggawa (Rapid Response Register, RRR) domin a agaza wa leburori da ke zaune a birane wa?anda matsalolin da annobar korona (COVID-19) ta haifar su ka shafe su kai-tsaye.

Ministar ta ?ara da cewa ana nan an kusa gama tsara kashi na biyu na masu amfana da shirin gwamnati na tallafa wa sana’o’i (wato ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’, GEEP) kuma za a sanar kwanan nan.

Ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta na kan bakan ta na ci gaba da aiwatar da Shirye-shiryen Ha?aka Rayuwa na ?asa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP), bisa ?udirin Shugaban ?asa na tabbatar da cewa an ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ?angin fatara da yunwa a cikin shekaru 10, musamman ta sabuwar hanyar sama wa matasa aikin yi da tallafa masu.”

A cewar Hajiya Sadiya Farouq, ma’aikatar ta ta dawo da shirin nan na ciyar da yara ‘yan makaranta (National Home-Grown School Feeding programme), ta ce ?alibai 9,196,823 ‘yan aji 1 zuwa 3 da ke makarantun firamare na gwamnati kowanne zai kar?i kwanon abinci mai gina jiki a dukkan makarantu 54,619 da ke fa?in ?asar nan.

Ta ce an fa?a?a shirin domin ya ha?o da ?arin yara miliyan 5 bisa umurnin da Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayar.

Ministar ta yi kira ga mutane 550,000 da aka ?auka a kashin ‘batch C’ na shirin N-Power da su garzaya su shiga gidan yanar ‘National Social Investment Management System’ (NASIMS) domin su shigar da bayanan su saboda su samu cancantar ?arshe ta cin gajiyar tsarin.

Ta ce kashi na biyu da ya ?unshi wasu ?arin mutum 500,000 su ma za a ?auke su nan gaba ka?an kamar yadda Shugaba Buhari ya umarci a ?auki mutum miliyan 1 a ?ar?ashin kashin ‘Batch C’.

Ministar ta ce: “Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa wannan ma’aikatar ta sake dawo da shirin nan na ciyar da yara ‘yan makaranta (National Home-Grown School Feeding programme)…

“Abin da wannan shiri zai haifar ya ha?a da samun ?arin yawan yaran da ake ?auka a makaranta, ?arin ingantaccen abinci ga yara, ha?aka tattalin arzikin al’ummar wajen da samar da aikin yi ta hanyar aikin masu dafa abinci mutum 103,028, ?ananan manoma 100,000 da sauran masu amfana irin su masu sufurin kaya da za a ?auka a fa?in ?asar nan.”

Related posts

Leave a Comment