Naira 385 Ya Kamata A Ri?a Sayar Da Litar Mai – Gwamnoni

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar gwamnonin kasar ta fitar bayan kammala taronta a ranar Laraba da daddare, wanda aka yi shi ta intanet. Sun yanke hukuncin ne bayan yin duba ga rahoton da wani kwamiti da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya jagoranta da ya goyi bayan janye tallafin mai daga gwamnati. A yayin gabatar da rahoton a wajen taron, Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata gwamnati na kashe tsakanin naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 kan tallafin man fetur, wanda ake sayar da litarsa…

Read More

Sabon Kamfanin Jirgin Saman Najeriya Zai Fara Aiki A Shekarar Badi – Sirika

Ministan Sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa sabon kamfanin jirgin sama mallakin gwamnatin tarayya, Nigeria Air zai fara aiki a farkon shekarar 2022 dake tafe. Sirika ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartaswar a Abuja a ranar jiya Laraba. Sirika ya ce an dade da shirin samar da wannan kamfani na kasa kuma zai fara aiki a farkon 2022, da farashi mai sauki fiye da kamfanoni masu zaman kansu. Sirika ya ce wannan sabon kamfanin jirgin zai…

Read More

An Dawo Da Dala Miliyan 700 Da Barayin Gwamnati Suka Jibge A Waje – Malami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya ce gwamnatin tarayya ta samo sama da dala miliyan 700 a cikin shekaru hudu na daga cikin kudaden da barayin gwamnati suka wawure suka jibge a ?asashen ?etare. Malami Ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wani taron da aka yi kan shige da ficen kudi ba bisa ka’ida ba da kuma samo su wanda hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta shirya. Ya ?ara da cewar kasashen da ke tasowa a Afrika…

Read More

An Shiga Tone-Tone Tsakanin Hadiza Bala Da Sanata Binta Garba

Dakatacciyar shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, Hadiza Bala Usman ta yi martani ga tsohuwar mamba a hukumar, Sanata Binta Garba wacce ta zargeta da wadaka da kudaden hukumar jim ka?an bayan dakatar da ita da aka yi. Sanata Binta Garba ta zargi Hadiza Bala Usman da assasa korarta daga hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA a kan yadda ta nuna rashin amincewarta da rahotannin shige da ficen kudade. A yayin martani, dakatacciyar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan NPA Hadiza Bala a wata takarda da ta sa hannu a…

Read More

Raina Masarauta: Sarkin Bauchi Ya Kori Wakilin Birni

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu, ya dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi, a kan rashin da’a ga sarki da kuma shigar alfarmar da yayi tamkar Sarki yayin hawan Sallah. Masarautar tace Abdullahi, wanda dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Bauchi a tarayya karkashin jam’iyyar PRP, an dade ana jan masa kunne a kan rashin da’a ga sarki da masarautar amma yayi kunnen kashi. A wata wasika mai kwanan wata 16 ga Mayun 2021 wacce aka aika ga dan majalisar a harshen Hausa, masarautar tace shigar da…

Read More

Babu Surukuntaka Tsakanin Buhari Da Kumo – Fadar Shugaban Kasa

Mai magana da yawun shugaban ?asa Malam Garba Shehu, ya ce Gimba Ya’u kumo da hukumar ya?i da cin hanci ta ICPC ke nema ruwa a jallo yanzu ba surikin shugaba Buhari ba ne. A cikin wata sanarwa da Garba Shehun ya fitar a ranar Jumma’a ya ce auren da ke tsakanin jami’in da ake zargin da ?iyar shugaba Buhari ya jima da mutuwa. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Garba Shehu na cewa koda ma auren bai mutu ba shugaba Buhari kamar yadda kowa ya san shi ba zai bayar…

Read More

Hukumar ICPC Na Neman Surukin Buhari Ruwa A Jallo

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ayyana neman Gimba Yau Kumo, surukin Shugaba Muhammadu Buhari ruwa a jallo kan zargin damfara ta Dala Miliyan 66 $66m. A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, Azuka Ogugua, mai magana da yawun hukumar ya ce ana neman Kumo da Tarry Rufus da Bola Ogunsola ruwa a jallo kan zargin ?annatar da karkatar da kudaden shirin samar da gidaje na ?asa. Kumo, tsohon shugaban Bankin Samar da Gidaje na Nigeria, ya auri, Fatima,…

Read More

An Zargi Hadiza Da Laifin Rashin Kunya Ga Manya

Rikicin cikin gidan da ake yi tsakanin shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na neman ya dauki wani irin yanayi. Inda Ministan ya yi ?ari akan zargin da yake yi wa tsohuwar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 a asusun gwamnati na CFR. Wani cikin ‘yan kwamitin da aka kafa ya shaida wa manema labarai cewa yanzu za su maida hankali ne a kan zargin Hadiza Bala Usman da laifin rashin kunya, da tsiwa ga manya. “Muna kallon…

Read More

EFCC Ta Kwato Dala Miliyan 153 A Wajen Tsohuwar Ministar Mai

Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta sanar da kwato $153m daga hannun tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke wadda ta tsere daga kasar zuwa Birtaniya a 2015. Jaridar Vanguard ta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun kwace akalla kadarori 80 da kudinsu ya kai $80m. “Muna fatan ganin lokacin da, watakila, za ta shigo kasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu dauka nan gaba. Tabbas ba mu…

Read More

An Kafa Kwamitin Bincikar Zunubban Hadiza Bala Usman

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken badakalar Hadiza Bala Usman. An dakatar da shugabar tashoshin jiragen ruwan ne sakamakon zarginta da ake da badakalar salwantar wasu kudade har N165 biliyan. Shugaban ayyukan da suka shafi teku, Suleiman Auwalu ne zai jagoranci kwamitin Sakamakon zargin badakalar wasu kudade da ake yi kuma ya kai ga an dakatar da manajan daraktan hukumar kula da hanyoyin shige da fice na ruwan kasar nan (NPA) Hadiza Bala Usman. Kwamitin…

Read More

Karayar Arziki: Gwamnatin Tarayya Za Ta Zaftare Albashin Ma’aikata

Ma’aikatar ku?i da kasafi da tsare-tsare ta ce an kafa kwamiti da zai yi nazarin yadda za a rage yawan ku?a?en da gwamnati ke kashewa musamman zabtare albashi da kuma rage yawan hukumomi. An ambato ministar ku?in Najeriya Zainab Ahmed na cewa, dole ne a fito da hanyoyin warware matsalar ?arancin ku?i da gwamnati ke ciki, lura da irin tsare-tsaren da ta ?auko da kuma lalurorin yau da kullum da ta ke magancewa kamar albashi da sauran ku?a?en tafiyar da gwamnati. Mai magana da yawun ma’ikatar ku?in ta Najeriya Yunusa…

Read More

Muna Dab Da Janye Tallafin Mai – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta kara jaddada wa yan Nijeriya cewa su shiryawa karin farashin man fetur saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki. Karamin ministan mai, Chief Timipre Sylva, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wajen yaye dalibai da basu kyaututtuka a jami’ar Patakwal, jihar Rivers. Sylva yace nan bada jimawa ba gwamnati zata zare tallafin man fetur, wanda a cewarsa wasu yan kasuwa ne kadai ke amfanaa da tallafin.

Read More

Kano Ce Kawai Ke Bin Tsarin Yaki Da Rashawa A Najeriya – Ganduje

Rahotanni daga birnin Kanon Dabo na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa a jihar Kano kadai ake yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda gwamnatin tarayya ke yi. Ganduje ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin tafiyar da dabarun yaki da rashawa na hukumar korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano. Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce wannan ne kwamiti mafi muhimmanci da za’a rantsar kan yaki da rashawa. “A jihar Kano kadai ake…

Read More

Ba Za Mu Iya Biyan Albashi Ba – Gwamnatin Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya ce gwamantinsa ba za ta iya biyan mafi karancin albashi ba. Yace yanzu gwamnatinsa na fama da biyan bashin da suka gada daga gwamnatin da ta gabata, na biyan albashi da kuma tafiyar da gwamnati ba ki daya. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya yi buda baki da mambobin kungiyoyin ‘yan kwadago 36 karkashin shugabancin NLC a Gusau babban birnin Jihar. An tabbatar da sabon mafikarancin albashi a Najeriya a matsayin doka a…

Read More

Muna Dab Da Kulle Layukan Da Ba A Yi Wa Rijista Ba – Pantami

Wa’adin da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta ?iba domin rajistar layin waya da lambar shaidar zama ?an ?asa ta NIN ya kusan cika. NCC ta tunatar da ?an Najeriya a shafinta na Twitter cewa ranar shida ga watan Mayu wa’adin da ta bayar zai cika. Rajistar ta shafi masu amfani da layukansu sadarwa su bayar da sahihiyar lambar shaidarsu ta NIN domin ha?a ta da layinsu. Kuma duk layin wayar da ba a yi wa rajista ba da lambar NINza a rufe shi.

Read More

Cin Hanci Ne Babbar Matsalar Najeriya – Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ba za ta taba ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta. Ganduje ya ce babu yadda za a yi kasar nan ta ci gaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a Najeriya. “Za ku yarda da ci idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba,” in ji Ganduje. Ganduje ya bayyana…

Read More

Za Mu Cigaba Da Ba Talakawa Tallafin Dubu 50,000 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da biyan kudaden tallafi ga gama garin mutane da ‘yan kasuwa a matsayin wani bangare na kokarin ta na rage mummunar tasirin kwayar cutar Corona a kan ‘yan Nijeriya, in ji kakakin fadar gwamnati a ranar Lahadi. Ana biyan kudaden ne a karkashin shirin gwamnatin na Survival Fund, wani bangare na shirin bunkasa tattalin arziki (ESP). Kunshin kudi tiriliyan N2.3 na ESP, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shi a ranar 24 ga Yuni, 2020. Kanana da matsakaitan masana’antu (MSME) suna da…

Read More

Shugaban ‘Yan Sanda Ya Bada Umarnin Janye Manyan Jami’an ‘Yan Sanda Daga EFCC

Mukaddashin sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin janye manyan jami’an ‘yan sanda masu mukamin Cif Sufuritandan da suke aiki tare da jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC. A wata wasika mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Idowu Omohunwa, wacce ya aike wa hukumar EFCC a ranar 15 ga watan Afirilu, mukaddashin sufeton ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan su dawo bakin aiki a ranar Laraba. Wasikar ta ci gaba da cewa ‘’Bisa umarni sufeton…

Read More

Majalisa Ta Amince Buhari Ya ?ara Cin Bashi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar majalisar dokokin tarayya ta amincewa mai girma Shugaban ?asa Buhari da ya ciyo bashi mai nauyi domin cigaba da ayyukan raya ?asa a Najeriya. Majalisar dattawa ta amincewa gwamnatin tarayya ta karbi sabon bashin dalar Amurka dala Biliyan guda da rabi $1.5bn, da Miliyan 995 €995m daga kasashen waje. A lissafin da aka buga, wannan kudi ya kama Naira Tiriliyan ?aya da digo 1 N1.1tr a kudin Najeriya. Sanatocin sun amince gwamnati ta karbi wannan bashi ne bayan kwamitin basussuka na majalisa…

Read More

Buga Takardun Kudi: Babu Gaskiya A Maganar Obaseki – Ministar Kudi

Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin da Gwamnan Jihar Edo ya yi cewa ta buga Naira biliyan 60 ta zuba cikin kudaden kasafin da ta ke rabawa a watan Maris. Ministar harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta karyata Gwamna Obaseki, a lokacin da ta ke wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa. Minista Zainab ta kara da cewa ikirarin Obaseki abin takaici ne kuma abin haushi, saboda ko kadan ba gaskiya ba ne. “Wannan ikirari da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi ni dai a bangare…

Read More