Ta Faru Ta ?are: An Ingiza Farouk Lawan Kurkukun Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban kwamitin binciken tallafin mai a majalisar wakilan Najeriya ya shiga gidan yarin Kuje a Abuja inda zai kwashe shekara 7 bayan yanke masa hukunci a ranar Talata, bisa samunsa da laifin badakalar kudade. 

An ruwaito cewa ba tare da ?ata lokaci ba aka tafi da Farouk Lawan gidan yarin Kuje bayan da kotu ta zartar masa da hukuncin ?aurin shekara bakwai a gidan yari.

Wata majiya da aka ambato ta ce zai ci gaba da zama a gidan yarin har zuwa cikar wa’adin da aka dibar masa. Sai idan kuma ya ?aukaka ?ara kuma ya yi nasara wanda zai sa a sake shi.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta sami Farouk Lawan ne da laifin karbar cin hancin dala 500,000 a wurin shararren dan kasuwa Femi Odetola domin wanke kamfaninsa daga bada?alar tallafin mai.

Related posts

Leave a Comment