Karancin Albashi: Har Yanzu Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar Kwadago Ba

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa harkawo yanzu ana jeka ka dawo akan takamaimai ?in mafi ?arancin albashi ma’aikata. Kungiyar kwadago ta bayyana dubu 250,000 a matsayin mafi ?arancin albashi, a gefe guda Gwamnatin Tarayya ta bayyana dubu 62,000 a matsayin mafi ?arancin albashi. Gwamnoni sun bayyana bazasu iya biyan Naira dubu 60,000 a matsayin mafi ?arancin albashi ba. Gashi wanki hula na ?o?arin kaiwa dare Kwanakin da kungiyar kwadago ta ?iba na komawa yajin aiki na karatowa.

Read More

Badakalar Biliyan 423: Mun Shirya Tsaf Domin Bincikar El-Rufai – EFCC

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzi?in ?asa zagon ?asa (EFCC) da kuma Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu zaman Kanta (ICPC) sun bayyana cewa har yanzu Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ba ta kai rahoto a hukumance kan zargin almundahanar Naira biliyan 423 da aka ce an tafka a zamanin tsohon Gwamna Nasiru Gwamnatin El-Rufai. “A watan Afrilu ne Majalisar Kaduna ta kafa wani kwamiti mai mutane 13 karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Henry Danjuma, domin binciken zargin karkatar da ku?a?en jihar da aka yi…

Read More

12 Ga Watan Yuni: Bama Goyon Bayan Duk Wata Zanga-Zanga – Kungiyar Matasan Arewa

images (71)

Kungiyar cigaban Matasan Arewa (AYCF) ta bayyana damuwa kan wasu rahotanni dake bayyana cewar wasu gungun jama’a na shirin gudanar da zanga-zanga domin haifar da rudani a bikin ranar dumukaradiyya ta 12 ga watan Yuni dake tafe. A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar ta matasan na Arewa Yerima Shettima ya fitar kuma aka rarraba wa manema labarai a Kaduna, ya yi tir gami da Allah wadai da duk wani shirin zanga-zanga da wasu za suyi musamman a ranar bikin 12 ga watan Yuni, wanda Najeriya ke murnar ranar…

Read More

An Sha Yi Mini Barazanar Kisa, Sakamakon Sukar El-Rufai – Shehu Sani

images (36)

Tsohon Sanatan Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani kuma ?an gwagwarmayar kwatar yanci ya bayyana cewa, sau ba adadi an yi masa barazanar kisa kawai don ya bayyana cewa, gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai tafi ko wace gwamnati sata a tarihin Jihar Kaduna.. Shehu Sani ya bayyana haka ne yayin wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a daren ranar Juma’a.. Haka zalika Sanata Shehu sani yayi rubuce-rubuce da dama akan irin satar da gwamnatin jihar Kaduna keyi a lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufai, a…

Read More

Muna Kokarin Saisaita Rayuwar Matsi Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Tinubu

IMG 20240429 WA0024(1)

Sugaban kasa Bola Tinubu ya sake jaddada cewa yana sane da halin matsin rayuwa da ‘yan ?asar ke fama da shi. Yayin da yake jawabi a wajen bikin ?addamar da aikin titin Guzape Lot II, a Abuja babban birnin ?asar ranar Asabar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin sau?a?a wa ‘yan ?asar halin matsin rayuwar da suke fuskanta. “Wannan lokaci ne mawuyaci a ?asarmu,Har yanzu muna ?o?arin saisaita tsarin tattalin arzikin ?asar, domin kawo sau?i da ingantuwar tattalin arzikin ?asarmu,” in ji…

Read More

Kaduna: Ba Mu Yi Mamakin Binciken El-Rufai Ba – PDP

IMG 20240331 WA0047

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara kan zargin tafka almundahana da Majalisar dokokin jihar ta yi wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai a shekaru takwas da ya yi a kan mulki. Jamiyyar adawa ta PDP a jihar ta ce ta san za’a rina, kuma za ta zura ido ta ga irin matakan da gwamnatin APC a jihar za ta dauka. Dan takarar gwamna a jam’iyar PDP a Kadunan a zaben 2023, Hon Isa Asiru Kudan, ya shaida…

Read More

Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’an Tsaro A Zamfara

Rahotanni daban-daban sun tabbatar da mahara sun kashe mutum 42 a farmaki daban-daban a yankunan Zamfara da Katsina. A Jihar Zamfara dai jaridar Daily Trust da wasu jaridu sun wallafa yadda aka bindige mutum 12 a ranar Alhamis a ?auyen Magarya, cikin ?aramar Hukumar Zurmi. Daga cikin mutanen da aka kashe, har da jami’in tsaro na Askarawan Zamfara da mutum hu?u. Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Mohammad Shehu, ya tabbatar wa Daily Trust kisan ‘yan sandan mobal ?in a Zamfara. Kwamishinan ya ce maharan kimanin su 300 sun mamaye ?auyen…

Read More

Saukar Da Farashin Kayayyaki ‘Yan Najeriya Ke Bukata Ba ?arancin Albashi Ba – PDP

IMG 20240226 WA0252

Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Delta Sunny Onuesoke ya ce, ?arin mafi karancin albashi ba shine maganin matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta ba, illa saukar da farashin kayayyakin abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a wani martanin da ya mayar dangane da yadda take kasancewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar nan. Onuesoke ya ce ?arin albashin ba zai magance matsalar tattalin arzikin kasar ba face ma ya ?ara dagula al’amurra.…

Read More

Karancin Albashi: Gwamnoni Za Su Iya Biyan Fiye Da 60,000 Idan Sun Rage Cin Hanci – NLC

FB IMG 1709098029346~2

Kungiyar ?wadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ?asar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ?arancin albashi, idan suka rage sata da cin hanci da rashawa da ku?in da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu. A ranar Juma’a ne dai ?ungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ?asar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ?arancin albashi ga ma’aikata ba. To sai dai a cikin martanin da ta mayar ?ungiyar ta…

Read More

Naira Dubu 60,000 Ta Yi Yawa A Karancin Albashi Ba Za Mu Iya Ba – Gwamnoni

IMG 20240608 WA0067(1)

Gwamnonin Najeriya 36 sun yi watsi da naira 60,000 a matsayin mafi ?an?antar albashi da gwamnatin tarayya ta ce za ta biya ma’aikatan ?asar tun da farko. Cikin wata sanarwa da ?ungiyar gwamnonin ?asar, ta wallafa a shainta na X, sun ce biyan 60,000 a matsayin mafai ?arancin albashi ba abu ne da zai ?ore ba. ”Kenan hakan na nufin da yawa daga cikin jihohin za su ri?a kashe duka ku?in kason da suke samu daga gwamnatin tarayya wajen biyan albashin ma’aikata, ba tare da komai ya ragu ba don…

Read More

Dan Bindiga Bello Turji Ya Karyata Labarin Kama Baleri

IMG 20240312 WA0021

Gawurtaccen ?an bindigar nan na Najeriya Bello Turji ya ?aryata i?irarin da sojojin Nijar suka yi na kama mashahurin ?an bindigar nan Baleri Fakai. Cikin wani bidiyo da ya kara?e shafukan sada zumunta, an ga Bello Turji, kewaye da maya?ansa ri?e da muggan makamai, ya nuna wani mutum da ya ce shi ne Balerin, ba wanda sojojin Nijar suka ce sun kama ba. Dama dai a makon da ya gabata ne Jaridar PRNigeria ta yi wani bincike da ta tabbatar da cewa mutumin da sojojin Nijar suka kama sunansa Kachalla…

Read More

Najeriya Za Ta Haramta Kiwon Dabbobi A Sarari

Dokar ta tsallake karatu na biyun ne bayan da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya bu?aci ‘yan majalisar da su ka?a kuri’ar amincewa ko kin amincewa, nan take kuma adadi mafi yawa suka amince da haramta kiwo a sararin. Bayan kammala ka?a kuri’ar majalisar ta bu?aci kwamitocinta kan harkokin noma, kasuwanci da zuba jari da kuma shari’a da su sake bibiyar dokar tare da dawo da ita majalisar don ?ar?arewa. Wa’adin wata guda ne aka baiwa kwamitocin don su kammala wannan aiki da aka basu mai cike da sarkakiya a Najeriya.…

Read More

Akwai Rufa-Rufa A Batun Janye Tallafin Mai – Atiku

IMG 20240224 WA0211

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da karkatar da ku?in gwamnati da sunan tallafin man fetur. Atiku ya ce ?in amincewar da gwamnatin Tinubu ta yi na bayyana ha?i?anin abin da take kashewa a kan tallafin man fetur ya nuna cewa tana karkatar da ku?a?en ne a sirri. Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, fadar shugaban ?asa ta ce matsayinta kan tallafi bai sauya ba. “Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire…

Read More

Dambarwar Masarautar Kano: Kotu Ta Dage Zama Zuwa 13 Ga Watan Yuni

FB IMG 1716698490096

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa a daidai ?arfe 2:35 na rana Alhamis ne Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Gya?i-gya?i, kan titin ‘Court Road’ ta ?age sauraren ?arar da dambawar masarautar Kano, zuwa ranar 13 ga Yuni. Kotun ta ce a koma ranar 13 ga Yuni domin ta tabbatar shin ta na da hurumin sauraren ?arar da tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba ?an’Agundi ya shigar, wadda ya ?alubalanci rushe masarautar Kano, lamarin da ya shafi har da rawanin sa. Gidan Radiyon Dala…

Read More

Neja: Tsoron ‘Yan Bindiga Ya Hana Ceto Mutum 50 Da Ramin Hakar Ma’adinai Ya Rufta Dasu

IMG 20240323 WA0041

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu akwai ?imanin mutum 50 da ke ?ar?ashin ?asa, wa?anda ramin ha?ar ma’adinai ya rufta da su, a yankin Galkogo, cikin ?aramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Wani kamfani ne mai suna “African Minerals and Industries Limited” ke aikin ha?ar ma’adinai a yankin, inda wurin ya rufta bayan saukar ruwan sama mai ?arfi, kuma ya turbu?e ?imanin mutun 50 a ?ar?ashin ?asa. Daga cikin wa?anda ramin ya rufta da su a ranar Lahadi, har da manajan kamfaninai suna Ibrahim Ishaku. An kuma ji…

Read More

Fetur A Arewa: ‘Yan Majalisa Sun Fusata Da Yadda Tinubu Ya Yi Watsi Da Aikin Mai Na Bauchi Da Gombe

IMG 20240226 WA0252

Mako ?aya bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara gagarimin aikin ha?o ?anyen mai a Jihar Ogun, Majalisar Tarayya ta nemi jin dalilin da ya sa aka dakatar da aikin ha?ar ?anyen man fetur a yankin Kolmani da ke Jihar Gombe da Bauchi. Cikin makon jiya ne dai Gwamnatin Tarayya ce za ta fara gagarimin aikin ha?o ?anyen man fetur a Jihar Ogun Gwamnatin Tarayya za ta fara gagarimin aikin ha?ar ?anyen man fetur a Jihar Ogun, kamar yadda ?aramin Ministan Fetur, Lokpobiri ya tabbatar. Ya ce hakan…

Read More

Da Dumi-Dumi: Majalisar Jihar Kaduna Ta Bankado Badakalar El-Rufai Ta Biliyan 423

IMG 20230808 WA0052(1)

Kwamitin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa domin binciken duk wasu kudaden, lamuni da kwangilolin da aka bayar a karkashin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya mika rahotonsa ga majalisar. Da yake gabatar da rahoton yayin zaman majalisar a yau ranar Laraba, shugaban kwamitin wucin gadi, Henry Zacharia, ya ce yawancin lamunin da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufai ba a yi amfani da su wajen yin hakan ba, yayin da a wasu lokutan ake samun su. ba a bi tsarin ba wajen samun lamuni. Da yake karbar rahoton,…

Read More

Juyin Mulki Ba Ya Faruwa Sai Da Sa Hannun ‘Yan Siyasa – Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban ?asa Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa juyin mulkin soja ba zai iya faruwa ba sai da hannun ‘yan siyasa. Abdulsalami, shugaban mulkin soja na karshe a Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Sun. KBC News ta ruwaito cewa an yi juyin mulki da dama a yammacin Afirka kwanan nan. A bara ne dai sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum bisa tafarkin dimokuradiyya. Abdulsalami ya shiga tsakani ne a madadin kungiyar ECOWAS ta yankin, bayan da aka kakabawa…

Read More

Rikicin Sarautar Kano: Sanusi Ya Samu Goyon Bayan Kungiyar Lauyoyin Najeriya

IMG 20240409 WA0041

Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wani babban taro da ta gudanar a jihar A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, NBA ta amince da Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar Sarkin Kano Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron ya ce har sai akwai karfin shari’a a ?asa ne al’uma ke iya yin rayuwa cikin salama A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince da Muhammadu Sanusi II…

Read More

Kamfanin Dangote Zai Samu Sama Da Miliyan Dubu Talatin A Karshen Shekara

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, kuma mutumin da ya fi kowa ku?i a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa zuwa ?arshen shekarar nan ta 2024, yana sa ran jimillar ku?in da zai ri?a samu a harkokin kasuwancinsa ya kai sama da dala miliyan dubu 30. A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta CNN, hamsha?in attajirin ya ce cimma wannan buri zai sa kuma kamfanin ya kasance ?aya daga cikin manya-manyan kamfanoni 120 na duniya. Attajirin ya ce, yadda ya sauya fasalin kamfanin ta yadda manyan…

Read More