Neja: Tsoron ‘Yan Bindiga Ya Hana Ceto Mutum 50 Da Ramin Hakar Ma’adinai Ya Rufta Dasu

IMG 20240323 WA0041

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu akwai ?imanin mutum 50 da ke ?ar?ashin ?asa, wa?anda ramin ha?ar ma’adinai ya rufta da su, a yankin Galkogo, cikin ?aramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Wani kamfani ne mai suna “African Minerals and Industries Limited” ke aikin ha?ar ma’adinai a yankin, inda wurin ya rufta bayan saukar ruwan sama mai ?arfi, kuma ya turbu?e ?imanin mutun 50 a ?ar?ashin ?asa.

Daga cikin wa?anda ramin ya rufta da su a ranar Lahadi, har da manajan kamfaninai suna Ibrahim Ishaku.

An kuma ji cewa wani mutum mai suna Kuta, wanda shi ne babban jami’in tsaro a wurin, ya ha?u da ajalin sa, yayin ?o?arin da ya yi ya ceto wasu da ramin ya rufta da su.

Daga baya an ceto mutum shida, wa?anda dukkan su sun ji raunuka, kuma aka garzaya da su wata cibiyar kula da lafiya a yankin.

An kuma ji cewa daga baya yayin da majiya ?arfi suka taru ana aikin ceto wasu da ke ?ar?ashin ?asar, sai wani gefe na ramin ya ?ara ruftawa, wanda hakan ya sa tilas masu aikin ceton tserewa a guje.

Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari dai mutum 50 na can ?ar?ashin ?asa, ba a san halin da su ke ciki ba. Hakan ya sa wasu na fargabar cewa sun ma rasa ran su a ?ar?ashin ?asa.

Jami’in Hul?a da Jama’a ma Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Hussaini Ibrahim, ya tabbatar da haka cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Litinin, a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya ce, “saboda yanayin dajin akwai ‘yan bindiga, ya sa ba a samun takamaimen labarin yanayin da ake ciki da wurin a halin yanzu. Ba za a ce an ceto ba har yanzu.”

Sai dai kuma ya ce an tura masu ceto domin su fito da su daga cikin ramun.

Ya kuma tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a yankuna biyu cikin Jihar Neja, a ranar Lahadi da dare.

Sun arce da mutum shida a ?auyen Malam Adogo, cikin ?aramar Hukumar Mashegun, sannan a Turgar Kawo kuwa sun kwashi mutum kamar 20. A Maza?ar Erena ta ?aramar Hukumar Shiroro kuwa, sun gudu da shanu ?aruruwa.

Related posts

Leave a Comment