Dambarwar Masarautar Kano: Kotu Ta Dage Zama Zuwa 13 Ga Watan Yuni

FB IMG 1716698490096

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa a daidai ?arfe 2:35 na rana Alhamis ne Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Gya?i-gya?i, kan titin ‘Court Road’ ta ?age sauraren ?arar da dambawar masarautar Kano, zuwa ranar 13 ga Yuni.

Kotun ta ce a koma ranar 13 ga Yuni domin ta tabbatar shin ta na da hurumin sauraren ?arar da tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba ?an’Agundi ya shigar, wadda ya ?alubalanci rushe masarautar Kano, lamarin da ya shafi har da rawanin sa.

Gidan Radiyon Dala F.M da ke Kano ya ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya mai zaman ta a Gya?i-gya?i, Kano, ?ar?ashin Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ta ?age zaman da ta fara na sauraron shari’ar da Aminu Babba ?an Agundi ya shigar, inda ya ke ?alubalantar Gwamnatin Jihar Kano akan batun kwaskwarimar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar masarautu.

A zaman kotun na yau Alhamis, lauyan wa?anda aka yi ?ara, Barista Mahamud Abubakar Magaji, ya bayyana wa kotun cewar, a zaman yau za a tattauna ne kawai akan batun hurumin kotun akan wannan shari’ar.
Sai dai lauyan mai ?ara, Barista Waziri ya shaida wa kotun cewar ba su rubuta martanin su akan wannan batu ba. A nan kotun ta umarce su da su rubuto martanin su cikin da awa ?aya.

Tun da fari dai Aminu Babba ?an Agundi ne ya shigar da ?arar gwamnatin Kano da Majalisar Dokoki, sakamakon gyaran fuska da majalisar ta yi wa Dokar Masarautun Jihar Kano ta 2019, inda sabuwar dokar ta rushe masarautu biyar da aka ?ir?ira kuma daga bisani Gwamnan Kano, Abba Kabir-Yusuf ya sanya hannu, tare da bayyana Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Rahotanni sun nuna cewa, yayin zaman, an girke jami’an tsaron ‘yan sanda da na DSS, wan?anda suka hana shiga harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.

Jami’an tsaron sun kuma hana kowa shiga harabar kotun, sai iya wa?anda suke da hurumi a shari’ar da ‘yan jarida.

Related posts

Leave a Comment