Mako ?aya bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara gagarimin aikin ha?o ?anyen mai a Jihar Ogun, Majalisar Tarayya ta nemi jin dalilin da ya sa aka dakatar da aikin ha?ar ?anyen man fetur a yankin Kolmani da ke Jihar Gombe da Bauchi.
Cikin makon jiya ne dai Gwamnatin Tarayya ce za ta fara gagarimin aikin ha?o ?anyen man fetur a Jihar Ogun
Gwamnatin Tarayya za ta fara gagarimin aikin ha?ar ?anyen man fetur a Jihar Ogun, kamar yadda ?aramin Ministan Fetur, Lokpobiri ya tabbatar.
Ya ce hakan ya zo ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke bu?atar ?arin ku?a?en shiga a ?angaren ?anyen mai da gas.
Lokpobiri ya ce za a fara aikin ha?ar a wasu wurare a fa?in Jihar Ogun, saboda Jihar ko tantama babu akwai ?anyen mai a cikin ta.
?aramin Ministan Fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin da ya kai ziyara Ofishin Gwamnan Jihar Ogun, a Abeokuta, babban birnin Jihar.
Lokpobiri ya kai ziyarar tare da manyan masu hannu a harkokin man fetur da gas daban-daban, cikin su har da Shugaban NNPCL, Mele Kyari.
Ya ce Jihar Ogun na ?aya daga ?angaren Dahomey Basin, wurin da ake da kyakkyawan zaton akwai ?anyen mai kwance ma?il a ?asa.
Ya ce sun kai ziyara Jihar Ogun ne domin su nuna irin gaggawar fara aikin wanda Gwamnatin Tarayya ke so a yi, domin ?ara samun hanyoyin ku?a?en shiga ta hanyar ?anyen mai.
Ya ce ?anyen mai ne hanya mafi saurin kawo wa Najeriya ku?a?en shiga masu tarin yawa.
A zamanin mulkin Buhari an ?addamar da aikin ha?ar ?anyen mai a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Sai dai kuma tun bayan ?addamar da aikin, har yau shiru ka ke ji babu labari kuma babu ?arin bayani.
Majalisa Na Neman Sanin Dalilin Dakatar Da Aikin Ha?o ?anyen Mai A Kolmani:
A ranar Laraba ce kuma Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta yi mata ?arin bayani a kan dalilan da suka janyo dakatar da ci gaba da aikin ha?o mai a yankin Kolmani da ke Gombe da Bauchi.
A watan Nuwambar 2022 ne, tsohon Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, ya ?addamar da aikin fara ha?o mai a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Sai dai shekaru biyu, bayan fara wannan aiki, ‘yan majalisar sun ce aikin ya tsaya.
Inuwa Garba, ?an Majalisar Tarayya ne daga Jihar Gombe da ya gabatar da koken, ya shaida wa BBC cewa a gaban jama’a da dama tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi al?awarin ci gaba da wannan aiki, hasali ma shi kan sa shugaban ?asa na yanzu ya na wajen. “To amma abin mamaki shi ne kullum aikin sai samun komawa baya yake.”
Ya ce, “A yanzu kamfanonin da ke aikin ha?o man sai tattara kayans u suke yi, suna barin wajen, kamar dai ?o?ari ake a yi watsi da wannan aiki.”
“Ni da kai na gudanar da bincike, don na je wajen na duba kuma muna magana da mutanen mu. NI fa ?an yankin ne domin daga jihar Gombe na ke, kuma wannan man da ake tonowa a tsakanin jihar mu ta Gombe da Bauchi wajen yake.” inji shi.
Inuwa Garba, ya ce wannan tono man da aka ce za a yi duk ?an yankin hankalin sa a tashe ya ke domin dakatar da aikin ko tafiyar hawainiyar da aikin ke yi ba ya yi musu da?i.
Ya ce, ”Wannan dalili ne ya sa na gabatar da ?udirin domin a ceto mu daga cikin halin da muke ciki ganin yadda ita kanta Najeriyar ke tafiya.”
?an Majalisar wakilan ya ce tunanin da mutane ke yi ko matsalar tsaro ce ta sa aka dakatar da wannan aiki, ba haka ba ne, domin batun matsalar tsaro gwamnonin yankin ko jihohi biyu na Gombe da Bauchi, sun ha?a kai da sarakunan gargajiyar yankin da ma ‘yan majalisun yankin don kawar da matsalar, kuma Alhamdulillahi babu wannan matsala, don haka ba rashin tsaro ne ya sa aka dakatar da aikin tono mai a wajen ba.
“Yanzu wannan waje na nan ana ta noma da kiwo babu wata matsala, mu dai kawai mun ga kamfanonin da ke wannan aiki suna ta kwashe kayan su suna tafiya aiki ya tsaya ai dole hankalin duk wani ?an yankin ya tashi.” Inji ?an majalisar tarayyar.
”Mu abin da muke so yanzu a yi shi ne Shugaban ?asa Bola Tinibu, ya tuna da al?awarin da ya yi a gaban mutane cewa lallai zai tabbatar da an ci gaba da wannan aiki na tono mai, don haka muna so yanzu mu ga an ci gaba da wannan aiki tare da sanya ku?in da zai isa a yi aikin don mu ma muna so mu ga an yi wani abin a zo a gani a ?angaren Arewa.”
