Saukar Da Farashin Kayayyaki ‘Yan Najeriya Ke Bukata Ba ?arancin Albashi Ba – PDP

IMG 20240226 WA0252

Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Delta Sunny Onuesoke ya ce, ?arin mafi karancin albashi ba shine maganin matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta ba, illa saukar da farashin kayayyakin abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a wani martanin da ya mayar dangane da yadda take kasancewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar nan.

Onuesoke ya ce ?arin albashin ba zai magance matsalar tattalin arzikin kasar ba face ma ya ?ara dagula al’amurra.

?an Najeriya suna yaudarar kan su ne kawai, amma abinda ake bukata a yanzu shine rage farashin kayayyaki. Idan za a kara albashi zuwa Naira Miliyan ?aya a yau, to haka ma farashin kayayyaki zai cigaba da ?aruwa.

Da zarar an ?ara mafi karancin albashi to haka farashi zai ?ara karuwa, Saboda Talakawan da ba Ma’aikatan Gwamnati ba da ke samar da kayan abinci kamar Tattasai, Doya da sauransu za su ?ara farashi.

A cewar Cif Onuesoke ” Karin albashi ba zai iya magance hauhawar farashin kayayyaki ba, saboda yadda ake samun karin albashi akwai karin kudin da ke yawo a tsarin. Yayin da aka samu yawaitar yawon ku?i a hannun Jama’a kuwa, to hakan zai ?ara haddasa hauhawar farashi, wannan ?an ?aramin lissafin tattalin arziki ne da ba kowa ke iya fahimta ba.

Ba Ma’aikatan Gwamnati ne ka?ai ke tafiyar da ?asar ba, Ma’aikatan Gwamnati kaso 14 ne cikin 100 kacal. Ma’aikatu masu zaman kan su kuwa ba duka bane za su iya biyan wannan adadin a matsayin albashi a kowane wata”

Ya ce abin da ‘yan Najeriya ke bukata a halin yanzu shi ne rage hauhawar farashin kayayyaki ta yadda ko da ma’aikaci yana karbar Naira dubu 20 a matsayin mafi karancin albashi to ya iya biyan kudin hayar gidan sa, da kuma biyan sauran bukatun sa cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wajen gina gidaje masu saukin kudi domin baiwa talaka tallafi da zai mora na tsawon rayuwarsu a matsayin hanyar rage hauhawar farashin kayayyaki.

Jama’a na bukatar ababen more rayuwa da za su rage wahalhalun da suke ciki, Abin da nake cewa shi ne Gwamnatin Tarayya da Gwamnonin Jihohi su kara kaimi ga ayyukan noma da gina gidaje masu dumbin yawa domin bada tallafi, da rage ku?a?en Asibiti.

Matsalarmu ita ce muna magani daban ciwo daban akan matsalolin ?an Najeriya, idan ka tambayi shugabanninmu kadada nawa ne za su samar da adadin rogo kaza? ba su sani ba, Amma sun iya cika baki akan al?alumman hasashe.

kowace karamar hukuma ya kamata ta samu kadada 80,000 na gonakin rogo, da Doya, da Masara, da Shinkafa da dai sauransu, sannan a gyara matatun mai, Me ya hana kasar gyara matatun Mai hudu da muke da su? har gobe Rashin gyara matatun Mai yasa muke shigo da shi daga waje, sannan kuma har gobe Najeriya ce kasa ta shida da tafi hako mai a duniya”

Karin mafi karancin albashin dai kari ne na Naira dubu biyu da Gwamnatin Tarayya tayi wanda tace zai zarce tayin farko na Naira dubu sittin.

Kungiyar kwadago kuwa ta rage dogon buri daga Naira dubu dari hudu da casa’in da hudu 494,000 zuwa Naira 250,000 duk wata.

Bangarorin biyu dai ba su kai ga cimma matsaya kan lamarin ba.

Related posts

Leave a Comment