Wasu ?anbindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza daya. An tattaro cewa an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a GRA Dustin Ma da misalin karfe 1:am na jiya Litinin. An kuma tattaro cewa ?an ta’addan sun mamaye al’umma da nagartattun makamai inda suka rika harbe-harbe. Da aka tuntubi kakakin rundunar ?ansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce rundunar ta na…
Read MoreKarancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Cimma Yarjejeniya Da Gwamnatin Tarayya
Rahotanni sun nunar da cewa, an cimma wannan matsayar yayin wani taro da kungiyar ta yi da kwamitin kasa kan mafi karancin albashin da aka fara da misalin karfe biyar na Yammacin Litinin din da ta gabata zuwa wajejen karfe 11 na dare. A cewar sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriyar George Akume kwamitin, zai rinka ganawa a kowacce rana tsawon mako guda domin lalubo bakin zaren warfare takaddamar da ke tsakanin gwamnatin da wakilan ma’aikatan. Hadakar kungiyoyin kodogon da gwamnatin Tarayyar dai, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka cimma.…
Read MoreRashin Matsaya: Kungiyar Kwadago Ta Shelanta Tsunduma Yajin Aiki Yau Litinin
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa akwai yiyuwar ayyukan tattalin arziki a Najeriya su tsaya cik sanadin yajin aikin da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC za su tsunduma a ciki daga yau Litinin. Kokarin da shugabannin Majalisar dokokin kasar suka yi domin sasanta bangarorin ya ci-tura. Bayan ganawar sa’o’i hudu da shugabannin Majalisar dokokin kasar da yammacin ranar Lahadi a Abuja, shugabannin kungiyar kwadagon sun ce babu gudu babu ja da baya game da yajin aikin gama gari da aka shirya ya fara ranar Litinin…
Read MoreSarakuna Biyu A Kano: Aminu Na Samun Kulawar Jami’an Tsaro, Sanusi Na Samun Kariyar ‘Yan Banga
A cigaba da yamutsin sarautar Kano da ake ta fama da shi inda sarakuna biyu kowa ke sarauta a Kano lamarin sai kara ?azanta ya ke yi. Sarki Aminu Ado da yake fadar Nasarawa, na samun tsaro ta musamman ne daga jami’an tsaro da aka turo su daga Abuja, shi ko, Sarki Sanusi da yake faradar rumfa, na samun kariya ce daga ?an banga da mafarauta da ke kare shi. Wannan yamutsi na sarautar Kano ta ?ai?aita sarautar mai ?inbin tarihi inda a Karon farko an samu sarauta mai asali…
Read MoreKarancin Albashi: Yajin Aiki Ba Gudu Ba Ja Da Baya – Kungiyar Kwadago
Kungyar ?arkashin shugabanta Ajaero ta bayyana cewa ba ta cimma matsaya ba game da yarjejeniyar ?arancin albashi da kuma rage tsadar wutar lantarki da ake fama da shi a ?asar. ” A zaman taron da muka yi, babu gwamna ko ?aya da ya halarci taron, haka kuma babu wani minista in banda ?aramar ministar Kwadago Nkiruka Onyejiocha. ” Haka nuni cewa maganar ?arin albashin ba ta ?a?a su da ?asa ba ko ka?an, ba ita ce a gaban su ba. Kungiyar ta ce tunda gwamnati ba ta ga amfanin zaman…
Read MoreEFCC Ba Ta Binciki Kwankwaso Ba – Shugaban Jam’iyyar NNPP
Shugaban jam’iyyar, NNPP, a jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya ce masu zagon kasa ba za su iya dakatar da makomar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabiu Kwankwaso ba. Dungurawa ya ce wadanda ke yakar Kwankwaso ne bayan rahotannin da ke cewa Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC na binciken sa. Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa na binciken Kwankwaso kan badakalar Naira biliyan 2.5. Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a Kano, jigon na…
Read MoreHajjin Bana: Alhazzan Najeriya Sun Koka Kan Zaftare Musu Kudin Guzuri
Mahajjatan Najeriya reshen birnin tarayya Abuja da yanzu haka ke kasar Saudiyya, sun gudanar da zanga-zanga inda suka nuna damuwa game da ba su dala dari biyu, a maimakon dala dari biyar da hukumar jin dadin alhazzan Najeriyar ta musu alkawarin ba su da farko a matsayin kudaden guzuri. Mahajjatan sun ce suna zargin akwai lauje cikin nadi game da wannan sauyi. Alhazan sun ce ba haka suka daddale da gwamnati ba kafin su tashi zuwa kasa mai tsarki. Daya daga cikin mahajjatan birnin tarayya Abuja da BBC ta tattauna…
Read MoreJinginar Da Filayen Jiragen Sama: Gwamnatin Tinubu Za Ta Binciki Buhari
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za a sake bibiyar kwangilar jinginar da Filayen jiragen sama guda biyu, wanda gwamnatin Buhari ta yi. Keyamo ya bayyana haka a Abuja, a taron Majalisar Zartaswa ta ?asa. “Za mu sake ko sabunta kwangilar jinginar da filayen jiragen biyu, domin a fito da komai a yi komai ke?e-da-?e?e. Ya ce har yanzu haka an dakatar da batun kafa Nigerian Air. Ya ?ara da cewa Jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines ne tsohon Ministan Hadi Sirika ya shafa wa…
Read MorePeter Obi Ya Ziyarci Helkwatar Jam’iyyar Labour Da Amincewa Da Sabbin ‘Yan Kwamitin Gudanarwa
?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya bi sahun dandazon magoya bayan jam’iyyar, inda ya ziyarci shagabannin jam’iyyar a helkwatar su da ke Abuja. Shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya kaddamar da sabbin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a karkashin jagorancin Barista Julius Abure, ya bukaci ‘yan kwamitin su sanya rayuwar ‘yan Nijeriya da ma kasa baki daya a sahun farko na dukkan al’amurran su. Peter Obi, ya ce ya kasance a sakatariyar jam’iyyar ne musamman don ya ziyarci shugaban ta, ya na mai shan alwashin ci-gaba…
Read MoreKarancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gamayyar ?ungiyoyin ?wadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya. Gamayyar ?ungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma’a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin. A farkon makon nan ne dai manyan ?ungiyoyin ?wadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi…
Read MoreShugaba Tinubu Zai Tsaga Najeriya Zuwa Tsarin Yanki-Yanki
A wani sabon salon jeka da halinka da Gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Tinubu ke shirin mika kudurin gaban majalisar wakilai da ta dattawa shine zai baiwa ko wani yanki yancin damar cin gashin kai wajen dogaro da abinda suke samu a yankinsu wajen rike kansu da kansu. Misali : mutanen da su fito daga yankin Naija Delta zasu dogara da ?anyen man fetur wajen dogaro da yankinsu. Mutanen da su fito daga yankin Legas da jihohin dake kunshe da Legas zasu dogara da kansu da abinda ake samu ta hanyar…
Read MoreSarautar Kano: Babban Alkali Ya Gayyaci Alkalan Da Suka Bada Umarni Masu Cin Karo Da Juna
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Alkalin Alkalai na ?asa (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci babban alkalin babbar kotun tarayya, da kuma babban alkalin babbar kotun jihar Kano kan wasu hukunce-hukuncen wucin gadi da suka bayar a masarautar Kano. Umarnin da ke cin karo da juna ya haifar da rashin tabbas da rudani a jihar. Tun da fari, babbar Kotun Tarayya da ke Kano, karkashin Mai Shari’a S. A. Amobeda ce ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar Kofar…
Read MoreShekara Guda A Mulki: Jam’iyyun Siyasa Sun Yaba Buhari Sun Sokin Tsarin Tinubu
?ungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa (CUPP) ta kushe gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekara daya da ya yi Kakakin kungiyar ya ce yan Najeriya sun sa ran samun sauki amma reshe ya juya da mujiya, wahala kawai suke sha ta kowanne fanni Har ila yau kakakin ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi Tinubu kokarin gudanar da mulki Kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa (CUPP) ta caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan rashin iya gudanar da mulki. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta fitar da bayani kan…
Read MoreRikicin Sarauta: Kotu Ta Umarci A Fitar Da Aminu Bayero Daga Karamar Fada
Mai Shari’a Aisha Adamu Aliyu ta babbar kotun Jihar Kano ta umarci kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kar?e ragamar mulki tare da fitar da sarki na 15, Aminu Ado Bayero. Umarnin na kotu ya nuna cewa, “An bayar da umarnin wucin gadi na hana mutane biyar da ake ?ara da duk wani mai ala?a da su, su daina gabatar da kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano da Karaye har zuwa lokacin da za a saurari ?arar da aka shiga a gaban kotu. “An bai wa kwamishinan ’yan…
Read MoreManufofin Tinubu Suna Da Kyau Sai Dai Ya Gamu Da Kurakurai – Obasanjo
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya soki yadda ake aiwatar da manufofin shugaba Tinubu, duk da cewa ya amince da muhimmancin su. Maganarsa tasa ya zo daidai da bukukuwan cikar Tinubu shekara guda kan karagar mulki. Obasanjo ya yi tsokaci ne na musamman kan wasu hukunce-hukuncen gudanarwa guda uku da suka hada da cire tallafin man fetur, yadda ake tafiyar da farashin canji, da Kuma martanin da sojoji suka dauka a Jamhuriyar Nijar. A cewar mai ba shi shawara kan…
Read MoreBabu Bukatar Warware Rikicin Masarautar Kano Da Karfin Iko – Malaman Kano
Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa, Majalisar malamai sun nuna damuwarsu kan abubuwan da ke faruwa a masarautar Kano inda suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ?aukar matakin da ya dace domin tabbatar zaman lafiya. Malaman sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai ?auke da sa hannun Majalisar Malaman karkashin jagorancin Shaikh Abdullahi Uwais Limanci. Sun ce abubuwan da ke faruwa a Masarautar na baya-bayan nan za su iya rikidewa zuwa babban rikici idan ba a yiwa tubkar hanci ba. Jihar Kano…
Read MoreSarakuna Biyu A Kano: Gwamna Abba Ya Bada Umarnin Kama Tsohon Sarki Aminu Bayero
Rikicin sarauta a Kano ya dauki sabon salo bayan da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke daga kujerar Sarkin Kano kwanaki biyu da suka wuce, ya koma birnin Kanon a ranar Juma’a da daddare. Aminu Ado Bayero tare da rakiyar wadansu magoya bayansa ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke birnin inda bayanai suka nuna cewa ya koma Kano ne domin ya shiga cikin gidan sarki bisa la’akari da cewa maganar cire shi na gaban kuliya. Sai dai gwamnatin jihar Kano…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Abba Mayar Da Sanusi Sarautar Kano
Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa da alama dai Muhammadu Sanusi II ba zai shiga gidan sarauta yanzu ba yayin da babbar kotun tarayya ta dakatar da gwamnatin Kano daga nada sabon sarki. Kotun Mai shari’a Liman ta bayar da umurnin hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Muhammadu Sunusi karagar mulki. Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa alkalin ya bada umarnin ne a daren ranar Alhamis duk da cewa a halin yanzu yana kasar Amurka. Wani mai rike da sarautar gargajiya, Sarkin Dawaki Babba, Aminu…
Read MoreMajalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Yi Wa Dokar Masarautu Gyara
Majalisar Dokokin Kano ta amince a dawo da dokar masarautu ta jihar domin yi mata kwaskwarima. Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi a ranar Talata. A shekarar 2019 gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautu ta jihar gyara inda aka ?ir?iro ?arin masarautu gudu hu?u masu daraja ta ?aya. Masarautun sun ha?a da Gaya da ?araye da Rano wa?anda aka ?aga darajarsu zuwa masu daraja da ta ?aya daidai da masarautar Kano. Sai kuma Masarautar Bichi da aka ?ir?iro, abin da ya sa…
Read MoreShekara Guda A Mulki: Tinubu Zai Binciki Ayyukan Ofisoshin Ministoci
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa anasa ran Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake duba yadda mambobin majalisar ministocin sa suka Gudanar da aikin su a cikin makon nan ko zaiye Garanbawul Gwamnatin dai za ta yi bikin cika shekara ta farko ne a mako mai zuwa, yayin da ministocin za su cika watanni tara kan karagar mulki bayan rantsar da su a Ranar 21 ga watan Agustan bara. “Shugaban kasa na iya karbar tantancewar aikin shekara ta farko na ministoci, masu ba da…
Read More



