Rahotanni daban-daban sun tabbatar da mahara sun kashe mutum 42 a farmaki daban-daban a yankunan Zamfara da Katsina.
A Jihar Zamfara dai jaridar Daily Trust da wasu jaridu sun wallafa yadda aka bindige mutum 12 a ranar Alhamis a ?auyen Magarya, cikin ?aramar Hukumar Zurmi.
Daga cikin mutanen da aka kashe, har da jami’in tsaro na Askarawan Zamfara da mutum hu?u.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Mohammad Shehu, ya tabbatar wa Daily Trust kisan ‘yan sandan mobal ?in a Zamfara.
Kwamishinan ya ce maharan kimanin su 300 sun mamaye ?auyen a kan babura.
“Sun kewaye jami’an tsaron mu suka bu?e masu wuta, nan take suka kashe ‘yan sanda bakwai, wasu da dama suka ji raunuka.
“Maharan ba su jin da?in yadda ‘yan sanda ke hana su yin ta’addancin su tsawon shekaru.
“Tun da aka jibge ‘yan sanda a yankin, ‘yan bindiga sun kasa kai hare-hare a yankin,” cewar Dalijan.
Amma ya ce za a ?ara girke jami’an ‘yan sanda a yankin.
Wani mazaunin yankin ya ce wajen ?arfe 5:10 na asubahi maharan suka kewaye ?auyen, lokacin da ake shirin yin Sallah.
Ya ce ‘yan bindiga sun ?one gidaje biyu da rumbuna da yawa, kuma sun saci ra?uma uku, shanu, tumaki da awaki. Amma ba su arce da mutum ko ?aya ba.
“Lokacin da mahara suka dira, mutanen ?auyen sun gudu cikin daji. Daga baya sun dawo an yi ?idayar gawarwaki 12, cikin su kuwa har da ta ‘yan sandan mobal bakwai.
“Kuma wannan ne karo na hu?u zuwan su ?auyen.
