Neja: Jama’ar Gari Sun Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar mazauna yankunan da ta’addancin ‘yan bindiga yayi kamari a yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi ta jihar sun nemi zaman lafiya da ‘yan bindiga.

Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindigan suka bukaci a yi yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin tare da sharadin cewa ba zasu dinga kai su kara wurin hukuma ba duk lokacin da suka ketare yankunansu.

Shugaban yankin Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya sanar da Daily Trust cewa tuni suka tura wakilai domin tattaunawa da ‘yan bindigan.

Ya kara da bayyana cewa, ‘yan bindigan sun bukaci Naira Miliyan domin sayen goro wanda zasu raba a tsakanin abokai da ‘yan uwa domin su san cewa an yi yarjejeniyar zaman lafiya da mutanen yankin, tare da alkawarin dawowar zaman lafiya idan aka kiyaye sharuddansu.

“A ranar Alhamis ‘yan bindigan sun kira mu inda suka bayyana mana cewa suna son a yi yarjejeniyar zaman lafiya. Don haka muka aika wakilai da zasu hadu da su kusa da dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Sun bukaci wakilanmu da su tsaya a Maganda sannan su je su dauke su. “A karshe, sun sanar da mu cewa mune silar fadansu da kuma yankunanmu. Sun ce duk lokacin da jama’a suka gansu suna wucewa da shanu, sai su yi musu kwanton bauna tare da fara kai musu hari.

Duk da kuwa shanun satan ba na jama’ar yankin bane don haka ba su ga dalilin da zai sa su hare su ba. A don haka ne suka yanke hukuncin daukar fansa.”

Sun kashe mana sama da maza 30. Bayan kashe maza, suna garkuwa da matanmu da kananan yara. “Sun ce bayan yarjejeniyar nan ta zaman lafiya, babu wata kungiyar ‘yan bindiga da za ta sake kai hari yankinmu kuma idan wata kungiyar tayi, zasu gano ta tare da daukar mataki.

Amma dole ne mu iya tattaro kudi koda kuwa bai kai yadda ake bukata ba. Muna bukatar taimakon su.” Kusherki ya kara da cewa, babban limamin Unguwan-Barmo da wasu mutum 20 da suka hada da mata 10 sun shaki iskar ‘yanci a ranar Talata a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyan.

“Sun ce idan kudi suke so, zasu cigaba da karbar kudin fansa. Sun ja kunnenmu kan mu daina kai musu hari duk lokacin da muka gansu amma idan muna son fada da su, sun shirya cigaba da fada har nan da shekara 10.”

Related posts

Leave a Comment