Gwamnonin Najeriya 36 sun yi watsi da naira 60,000 a matsayin mafi ?an?antar albashi da gwamnatin tarayya ta ce za ta biya ma’aikatan ?asar tun da farko.
Cikin wata sanarwa da ?ungiyar gwamnonin ?asar, ta wallafa a shainta na X, sun ce biyan 60,000 a matsayin mafai ?arancin albashi ba abu ne da zai ?ore ba.
”Kenan hakan na nufin da yawa daga cikin jihohin za su ri?a kashe duka ku?in kason da suke samu daga gwamnatin tarayya wajen biyan albashin ma’aikata, ba tare da komai ya ragu ba don gudanar da wasu ayyuka”, in ji sanarwar.
Gwamnonin sun ce daga ?arshe wasu jihohin za su ?are da cin bashi don biyan ma’aikata a kowane wata.
”Wannan ba abu ne da zai amfani ?asarmu ba, ciki har da ma’aikata”, in ji gwamnonin.
A ranar Talata 4 ga watan Yuni ne ?ungiyar ?wadago ta janye yajin aikin da ta fara a farkon makon bayan wata ganawa da wakilan gwamnatin tarayya.
Gwamnatin tarayyar dai ta al?awarta biyan sama da naira 60,000 a matsayin mafi ?an?antar albashin.
?ungiyoyin ?wadagon dai sun bu?aci gwamnatin tarayya ta biya naira 494,000 a matsayin mafi ?arancin albashin.
To sai dai gwamnonin ?asar sun yi kira ga duka ?angarorin biyu, musamman ?ungiyoyin ?wadago su yi la’akari da halin tattalin arziki da ?asar ke ciki wajen amincewa da abin da za a iya ci gaba da biya, da zai da?a?a wa duka ?angarorin biyu.
