Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce bai damu da yun?urin da majalisar dokokin jihar ke yi na bincikar gwamnatinsa ba. El-Rufai ya yi nuni da cewa mai yiwuwa gwamnatin ba za ta yi nasara ba. Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan a wani taron Sallah da ya yi da mu?arrabansa a ranar Talata 18 ga watan Yunin 2024. El-Rufai ya kuma shawarce su da su guji yin cacar baki da hadiman gwamnan, inda ya yi hasashen…
Read MoreAn Shawarci Tinubu Ya Kau Da Kai Kan Rikicin Sarautar Kano
Injiniya Buba Galadima yace Matu?ar Tinubu bai tsame bakinsa akan sha’anin Kano ba, zai kawo masa silar rasa kujerarsa ta shugaban ?asa, Buba yakar cewar Idan har rikicin Boko Haram zai ?auki gwamnati shekaru goma sha uku zuwa goma sha hudu kafin a shawo kan al’amarin, ya kamata gwamnatin tarayya tayi taka-tsan-tsan da rikicewar jihar Kano. Buba Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Arise tayi da shi a daren ranar Litinin.
Read MoreBabu Wanda Ya Isa Ya Yi Mana Barazana Kan Rikicin Sarautar Kano – Kwankwaso
?an takarar shugaban kasan Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya da biye shawarar wasu makiyan Kano don wargaza zaman lafiya da aka san jihar. Da yake tsokaci kan rikicin Sarautar Kano, Kwankwaso ya zargi hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya da goyon baya Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, sabanin aikinsu na tabbatar da tsaro da kuma doka da oda a jihar. A cewarsa, “Muna da dimbin mabiya saboda jama’a sun amince da mu kasancewar muna tare da su, kuma a shirye gwamnain NNPP…
Read MoreCin Ajiyayyen Dafaffen Abincin Da Ya Haura Kwanaki Uku A Firij Na Iya Haifar Da Mutuwa – NAFDAC
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci ta Kasa, NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shawarci ‘yan Najeriya da su kaurace wa ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki uku. An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola, ya sanya wa hannu a ranar Talata. Hukumar ta yi gargadin cewa dafaffen abincin da aka ajiye a cikin firij na kwanaki zai fuskanci gurbacewar cututtuka da za su iya kaiwa ga mutuwa. Wasu sassan sanarwar sun bayyana…
Read MoreTalauci Da Wahalar Rayuwa Matsalar Duniya Ce Ba Najeriya Kadai Ba – Tinubu
Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayanin cewa matsalar talauci ba ?an Najeriya ka?ai ta shafa ba Shugaba Tinubu ya bayyana cewa akwai talauci da wahala a ?asar nan amma hakan matsala ce wacce ta shafi dukkanin duniya ba Najeriya ka?ai ba Ya yi nuno da cewa dole ne a magance matsalar ayyukan ?an bindiga da ta’addanci domin manoma su samu damar noma abinci a gonakinsu Shugaban ?asa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba ?an Najeriya ne ka?ai ke fuskantar talauci a duniya ba. Shugaban ?asan wanda ya amince…
Read MoreGwamnatin Buhari Ce Silar Jefa ‘Yan Najeriya Mawuyacin Halin Da Suke Ciki – Fadar Shugaban Kasa
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, gwamnatin tarayya karkashin shugaba Tinubu ta ?ora alhakin wahalar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki kan tsohuwar gwamnatin Shugaban ?asa Buhari. Mai ba Shugaban ?asa shawara kan ya?a labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa ya zamarwa tsohuwar gwamnati dole ta ?auki alhakin halin da ?an Najeriya ke ciki a yanzu. Bayo Onanuga na mayar da martani ne kan wata ma?ala da jaridar New York times da ake wallafawa…
Read MoreBarka Da Sallah: Shugaban Kasa Ya Bukaci Musulmi Su Sanya Najeriya Cikin Addu’a
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sako na musamman yayin da al’ummar Musulmi ke shirin fara hidimar babbar sallah. Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga Musulmi kan sadaukarwa domin kowo nasara da cigaban ?asa. A cikin wani sako da jami’in yada labaran fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nuni da cewa babbar sallah tana da ala?a da sadaukarwa ne da aka yi a baya. Saboda haka ya bu?aci yan Najeriya da su nuna sadaukarwa domin…
Read MoreMulkin Dimukuradiyya Ya Fi Tsarin Kowane Irin Mulki – Shugaba Tinubu
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mai girma Shugaban ?asa Tinubu ya bayyana tsarin mulkin Dumukaradiyya a matsayin tsarin da ya fi kowane irin tsarin mulki a fa?in duniya. Shugaban ya bayyana hakan ne a wani ?angare na jawabin da ya gabatar a bikin ranar Dimokuradiyya ta bana a fadar shugaban kasa dake Abuja. Tinubu ya ?ara da cewa mulkin dimukuradiyya ne kacal a duniya ya ba jama’a damar za?en wanda suke so ya jagorance su bisa ga yarjejeniya ko al?awurran da aka yi a…
Read MoreMulkin Tinubu: Najeriya Ta Talauce Amma ‘Yan Siyasa Na Fantamawa – Soludo
Da yake jawabi a wajen wani taro da ‘The Covenant Nation’ ta shirya domin saukaka ci gaban kasa, Soludo ya koka da cewa al’ummar kasar su na cikin wahala amma gwamnati da ?an siyasa na ci gaba da rayuwar fantama wa da yin rayuwar ?arya da hakkin talakawan da su ka za?e su. Gwamnan ya ce a matsayin hanyar dakile rikicin da ke tasowa kada ya ta’azzara, ya kamata a sanya masu rike da mukaman siyasa a kan mafi karancin albashi na kasa. Soludo ya bayyana cewa ?an Najeriya na…
Read MoreEl-Rufai Ya Kashe Kaduna Fiye Da Yadda Ake Zato – Henry Marah Sakataren Kwamitin Binciken El-Rufai
An bayyana tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i a matsayin wata annoba da ta fa?a wa Jihar Kaduna a tarihin kafuwar jihar, bisa la’akari da yadda tsohon Gwamnan ya yi wa Jihar rugu-rugu da tarin basussuka na fitar hankali. Mai magana da yawun Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa domin bincikar bada?alar ku?a?e da tsohon gwamna El-Rufa’i ya yi, Honorabul Henry Marah ya bayyana haka, a yayin tattaunawarshi da ‘yan jaridu a ofishin sa na majalisar dokokin jihar Kaduna. Honorabul Henry ya kara da cewar a binciken…
Read MoreFina-Finai: Muna Shawartar ‘Yan Mata Masu Niyyar Shiga Harkar Fim Su Dakata – Maishadda
Labarin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa daya daga cikin masu shirya fina-finai a arewacin najeriya Abubakar Bashir Maishadda yace, a kullum yana karbar kiraye-kiraye da sakonni sama da guda hamsin daga mata daban daban dake son shigowa kannywood da sunan zasuyi film, ni kaina nakan basu shawara su je suyi aure ko karatu, amma ni dai na daina daukan sabbin fuska acikin fina-finaina, sannan su kansu wadanda suke cikin masana’antar, a kullum addu’a na da fatana garesu shine, da sunyi film daya biyu sunyi suna, suje…
Read MoreKarancin Albashi: Babu Wata Yarjejeniyar Da Muka Yi Da Gwamnatin Tarayya – Kungiyar Kwadago
Kungiyar Kwadago ta ?asa NLC ta mayar da martani kan jawabin ranar dimokuradiyya da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi, inda ya bayar da tabbacin karin albashi mafi karanci ga ma’aikata, inda ya ce ya kasa bayar da kyautar da ake sa rai a ranar 12 ga watan Yuni. Shugaban kungiyar ta NLC, Kwamared Prince Adewale Adeyanju wanda ya mayar da martani a madadin kungiyar ya ce mai yiwuwa shugaban kasar ya ba da labarin wasu sassa na tarihin tafiyar dimokuradiyyar mu daidai, amma a bayyane yake cewa an yi…
Read MoreHajjin Bana: An Shiga Damuwa Kan Tsananin Zafi A Saudiyya
Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ?asar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ?aruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji. Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a. Hukumomin ?asar kan yi tanadin na’urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta. Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara
Read MoreKu Kara Hakuri Ina Sane Da Halin Kuncin Da Ku Ke Ciki – Tinubu Ga ‘Yan Najeriya
A sakon sa na bikin ranar dimokiradiya ta bana, wadda ke nuna yadda aka kwashe shekaru 25 ana gudanar da ita ba tare da samun targade ba. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri game da halin matsin da suka samu kan su, wanda yace yana sane da shi, kuma nan gaba kadan za su dara. Shugaban ya kuma bayyana shirin gabatar da kudirin yiwa sabuwar dokar albashi gyaran fuska domin amincewa da sabon karin da ake tattaunawa a kai. A yayin da ya ke jawabin,…
Read MoreTinubu Zai Yi Gagarumin Garambawul A Majalisar Ministoci
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kammala shirye-shiryen yin garambawul ga majalisar ministocinsa nan ba da dadewa ba, wanda zai hada da nada sabbin ministoci da kuma samar da sabuwar ma’aikatar, kamar yadda KBC News ta tattaro. Sabuwar ma’aikatar za ta kasance ne na raya dabbobi, wanda ya zuwa yanzu a karkashin ma’aikatar noma da raya karkara, da nufin tafiyar da tsarin kula da kiwon dabbobi na Gwamnati. Babban tsarin kula da dabbobin Najeriya da aka kaddamar a watan Agustan shekarar da ta gabata, an kafa shi ne domin jagorantar…
Read MoreKaduna: Shugaban ?ungiyar Masu Sayar Da Motoci Ya Sha Alwashin Kai Kungiyar Gaba
Shugaban ?ungiyar masu sayar da motoci ta ?asa reshen Jihar Kaduna Alhaji Aminu Ibrahim ?an ?a?alo ya bayyana cewar babban kudurin da ya sa a gaba shine zamanantar da tsarin ?ungiyar zuwa ga mataki na cigaba. Aminu ?an ?a?alo ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da da ya yi da manema labarai kan kudurorin Shugabancin sa a sakatariyar ?ungiyar dake garin Kaduna. ?an ?akalo ya ?ara da cewar ?ungiyar tasu tana cikin wani yanayi na rashin wayewar zamani a tsawon lokaci kusan shekaru 40, inda ya sha alwashin ?ora…
Read MoreRanar Dimokuradiyya: Tinubu Ya Jadadda Aniyar Gwamnati Na Fitar Da ‘Yan Najeriya Daga Kunci
A yayin da ya ke jawabin, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa gwamnatinsa na dab da kai karshen maganar sabon mafi ?arancin albashi., Ya ce idan komai ya kammala, zai mika wa majalisar tarayyar kasar domin su amince da shi wanda ya ke da yakinin zai zama mafi dacewa ga ma’aikatan. A cewar shugaban kasar: “Ina sane da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya. Sama da shekaru ya kamata a gyara tattalin arzikin kasar saboda lalacewa da rashin makoma. “Tun bayan hawan mu mulki, mun aiwatar…
Read More‘Yan Majalisa Sun Bukaci A Mayar Da Wa’adin Shugaban Kasa Da Gwamnoni Shekaru Shida-Shida
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wasu gungun ?an majalisar wakilai na neman a sauya kundin tsarin mulkin kasar na 1999 domin share fagen zaben shugaban kasa a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan. Suna kuma son a yi wa Kundin Tsarin Mulki gyara domin ya tanadi “wa’adi guda na shekaru shida na shugaban kasa da Gwamnonin Tarayyar Najeriya. Da ya ke jawabi a madadin yan majalisar a yau Litinin a Abuja, mamba mai wakiltar mazabar Ideato South/Ideato North, Jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, ya ce,…
Read MoreNajeriya Ta Goyi Bayan Tsagaita Wuta A Gaza
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan Harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya yi kira da a ?auki matakin gaggawa Domin dakile munanan hare-haren da ake kai wa a rikicin I$ra’ila da Falasdinu. Ambasada Tuggar ya kuma tabbatar da goyon bayan Najeriya ga shawarwarin tsagaita wuta na shugaba Joe Biden. “Ya kamata shugabannin duniya da daukacin al’ummar duniya su amince da kudurin tsagaita bude wuta na Biden don kara kaimi wajen warware rikicin cikin gaggawa da kuma dakatar da mummunan tashin hankali a…
Read MoreYobe: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Dukkanin Kananan Hukumomin Jihar
Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 17 da aka kammala zaben kananan hukumomin jihar. Haka kuma jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun kansiloli 178 na jihar. Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe, YOSIEC, Dr Mamman Muhammad, ne ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Damaturu a ranar Lahadi. “APC ta lashe dukkan kujeru 17 da kansiloli 178 a zaben kananan hukumomin jihar,” in ji shi. Ya kara da cewa hukumar ta karba, ta duba, ta tantance tare da amincewa da sakamakon kowanne…
Read More



