Kungiyar ?wadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ?asar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ?arancin albashi, idan suka rage sata da cin hanci da rashawa da ku?in da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu.
A ranar Juma’a ne dai ?ungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ?asar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ?arancin albashi ga ma’aikata ba.
To sai dai a cikin martanin da ta mayar ?ungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ?arancin albashin.
”Koda nawa ne mafi ?arancin albashi ba ma naira 60,000 ba, in suka rage ku?in da suke kashewa wajen gudanar da gwamnati, sannan suka rage cin hanci da rashawa to za su iya biya domin tabbatar da walwalar ma’aikata”, in ji sanarwar.
A ranar Juma’a ne bayan wata ganawa da wakilan gwamnati ?ungiyar ?wadagon ta bu?aci gwamnatin tarayya ta biya naira 250,000 a matsayin maf ?arancin albashi.
