Rahotanni daga birnin Katsina na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ?an bindiga sun za?i su rika kashe mutane ‘suma bai dace a bar su da rai ba’.
Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ?an bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.
Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Wadanda suka hallarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar da wasu da dama.
Sarkin ya ce tunda ?an bindigan sun yanke hukuncin su rika kashe mutane suma bai dace a bar su da rai ba, mutuwa ta cancance su mafi muni.
Sarkin ya kuma koka kan yadda ake jinkiri wurin hukunta ?an bindiga yana mai cewa ‘hakan baya zama gargadi ga wasu ?ata garin’ A cewar Sarkin, ya kamata gwamnati a dukkan matakai su tashi tsaye don ganin an hukunta yan bindiga yana mai cewa bai dace mutum ya zama ?an fashi ba da sunan nuna rashin jin dadin sa.
Yan bindigan dai sun addabi mutane a yankunan arewa maso yamma, suna garkuwa da mutane suna karbar kudi tare da kisa da ?one-?one.
Wasu gwamnonin jihohin kamar Katsina, Zamfara, Sokoto sun dauki matakan toshe layukan waya, hana sayar da fetur a jarka, hana cin wasu kasuwanni don da?ile ?an bindigan.
Sarkin ya kuma soki mutane irin su Sheik Ahmad Gumi da ke kira ga gwamnatoci su tattauna da ‘yan bindiga har ma su duba yiwuwar yi musu afuwa da basu tallafi.
