Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane uku da ake zargi da yin fashi wajen shiga gidajen al umma a cikin karamar hukumar yola ta kudu dake jahar Adamawa.
Rundunan ta baiyana haka ne a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan D S P Suleiman Yahaya Nguroje, wanda aka rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan ya cigaba da cewa an samu nasaran kama mutanen ne biyo bayan bayanain sirri da suka samu daga mazauna garin na yola dangane da ahiga gidaje da mutanen keyi da da dare.
Hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Muhammed Ahmed Barde ya bada umurnin bincike kan wadanda ake zargin kuma yace da zaran sun kammala bincike zasu gabatar da su gaban kotu domin su fuskanci shariya.
Kwamishinan yan sandan yan sandan ya kuma tabbatarwa gwamnati da ma al umman jahar Adamawa rundunan a ahirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya.
Ya kirayi al umma jahar da sukasance ma su baiwa Jami an yan sandan hadin kai da goyon baya domin ganin sun samu nasaran kawar da dukkanin aikata laifuka a tsakanin al umma baki daya.
Rundunan yan sandan ta kuma gano wayoyin hanu da kayakin sawa, dama wasu kayakin a wurin wadanda ake zargin.
