Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar ‘yan shi’a mabiya Zakzaky ta yi zargin cewa an kashe mabiyanta lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa jerin gwanon zanga-zangar da suke yi na ranar arba’in a ranar Talata a Abuja
Haka kuma kungiyar ta ce an jikkata mabiyanta da dama sannan wasu da yawa ba a san inda suke ba.
Sai dai ‘yan sanda sun ce babu wanda ya rasa ransa a hargitsin.
Daruruwan mabiya shi’a sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun auka musu a yayin da suke gudanar da Zanga-Zangar arba’in don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah Sayyiduna Hussaini ya shiga a karni na bakwai a Karbala, wanda a cewarsu duk shekara suna yi.
Sun bayyana haka ne lokacin da suka kira wani taron manema labarai a Abuja, bayan faruwar lamarin.
Sakataren Kungiyar ‘yan shi’an Malam Abdullahi Muhammad Musa ya shaida cewa, suna kan hanyar shiga cikin Abuja a dai-dai Gwarimpa, sai suka ji an jefa musu barkonon tsohuwa.
Bugu-da-kari Abdullahi ya ce akwai wadanda ba a gansu ba, inda suke kan tattara yawan wadanda suka batan, ciki har da wadanda ba su ji ba su gani ba.
Sannan ya ce fiye da mutum goma sha daya sun jikkata yayin Zanga-Zangar.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin Abuja Josephine Adeh, ta ce ba haka lamarin yake ba, hasalima mabiya shi’a ne suka far musu, amma ta ce sun kama wasu daga cikinsu da dama dauke da makamai.
‘Yan kungiyar dai sun sha yin artabu da jami’an tsaro a ‘yan shekarun nan a fadin tarayyar Najeriya.
