Obasanjo Ya Karbi Kwangilar Kawo Zaman Lafiya A Afirka

Rahotannin dake shigo mana yanzu na bayyana cewar Shugaban kungiyar kasashen Afrika ta AU, ya hada Olusegun Obasanjo da aikin kawo zaman lafiya a cikin fa?in nahiyar Afirka gaba ?aya.

An ruwaito cewa tsohon shugaban kasar Najeriya zai yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da lumana a gabashin Afrika.

Olusegun Obasanjo ya isa birnin Addis Ababa ta kasar Habasha domin fara aikin da aka ba shi na babban jakadan kungiyar AU a kasashen da ke yankin.

Ana sa rai Obasanjo wanda yana cikin dattawan Afrika ya kawo karshen tashin-tashinan da ake yi a kasashen Afrika ta gabas inda ake fama da yawan rikici.

Kasashen da aka ba Obasanjo dawainiyar kawo zaman lafiya sune; Djibouti, Eriteriya, Habasha, Somaliya, Kenya, Sudan, Sudan ta kudu da kuma Uganda.

Rahoton yace jawabin da ya fito daga bakin shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, yace Obasanjo zai shiga, ya fita domin kawo karshen rigingimun. Kungiyar AU tana ganin Obasanjo yana da kwarewar da zai sa rigingimun yankin su zama tarihi.

“Babban wakilin zai karfafa tattauna wa da ‘yan siyasa da sauran masu ruwa-da-tsaki domin a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”

Tsohon shugaban kasar ya shaida wa manema labarai cewa ya isa garin Addis Ababa a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, kuma ya ma soma aikinsa.

Tuni har Obasanjo ya zauna da shugabannin kasar Habashan da wasu jagororin AU. Sannan zai shiga ganawa da shugabanni daga Sudan, Kenya da Somaliya.

Related posts

Leave a Comment