An Bukaci Matasan Nijeriya Su Kara Yin Karatun Ta-Natsu Don Kaucewa Fadawa Munanan Hali Musamman a Wannan Lokaci da Muke ciki.
Wannan Kira Ya Fitone Daga Bakin Wani Matashi Mai Suna Abdulwahid Umar Haza A lokacin Da Yake ganawa Da Manema Labarai a Kaduna.
Binhaz ya ce Halin da Matasa Suka Tsunduma Kansu Na Shaye-Shaye ne Ya Kara Jefa Matasan Cikin Halin Kaka ni Kayi, Inda ya Kara da cewa Akwai Bukatar Matasan Su Rungumi Wata Sana’a Domin Su Dogara Da Kansu Basai Sun Jira Gwamnati ba.
Daga Karshe Abdulwahid Ya Jinjinawa Jamian Tsaron Nijeriya Ganin Yadda Suke Kokarin Kawo Karshen Yan Taadda Musamman a Arewacin Nijeriya, Sannan Yace Ya Kamata a Dauki Matasan da suke zaune ba aikin yi aikin soji da na ‘Yan Sanda Da Sauran Jami’an Domin Rage Masu Zaman Kashe Wando.
