Bauchi: Jama’ar Birshin Fulani Za Su Yi Barci Da Minshari – Kakakin ‘Yan Sanda

Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi ta tashi haikan wajen dakile ayyukan yan’tadda da masu garkuwa da mutane a yankin Unguwar Birshin Fulani da kewayen ta da ma sauran al’umman a sassbanbance titin hanya Bauchi zuwa Dass a yan’ kwanakin da suka wuce

Yace yanzu haka sun tsaurar matakan tsaro a yankin ta wajen samar da motoci masu sulke da zirga zirga na awa ashirin da hudu 24, tare da hadin gwiwa da sauran Jami’an tsaro da mutanen gari, kai sumame a kowani lokaci, lungu da sako na yankin kana da sa’ido a kangwayen gine gine a cikin Unguwan da kuma binciken kwakwaf a kan hanya na musamman domin zakulo masu aikata wan nan mummuman aiki na satar Jama’a da kisan gilla.

Wakil ya kara da cewa tuni rundunar ta saurari koke koken da Jamar yankin sukayi, don sama masu mafita daga matsalar tsaro a yankin, ya tabbatar da cewa Yan’sanda suna iya kokarinsu don kama wadanda suke da alaka kowace iri date ba rana don kare rayuka da dokiyoyin mutane, saboda haka yanzu zasu yi barchi da idanun su biyu a kulle

Bugu da Kari yace. “Jami’an Yan’sanda an basu motoci don karin karfi gwiwa Amma in akayi la’akari da yadda suke amfani da babura, wasu motocin ba zasu iya shiga wan nan wuri ba” dole sai an matsa kaimi sosai”.

Har’ila yau Ahmed Wakil, yayi tsokaci kan yanayin tsaro a unguwar, yace Yan’sanda kullun suna sauraron bayanan jama’a saboda haka baza muyi kasa a gwiwa ba, Kuma yaja kunne mutane su guje mayar da matsalar tsaro a cikin siyasa da bashi da tushe bale makamai, Kuma ba zai amfanar da kowa ba sai dai rudani.

“Wani kawai ya tashi rana tsaka yace babu tsaro a yankin, Kuma jami’an tsaro basu kula ba, wan nan ba gaskiya bane, Kuma ba yi masu adalci ba, yace che-che kuce ma bai taso ba a wan nan batu”. Ya jaddada.

Kana Kakakin ya kirayi al’umma a ko ina da zarar sunji motsin batagari, karsu yi jinkirin sanar da Yan’sanda don kare rayuka da dukiyoyi daga salwanta, yace kamata yayi mutanen su godewa.jami’an Yan’sanda ba korafe korafe ba, wadanda basu da tushe balle makama

Yayinnda yake Kari haske kam.garkuwa da akayi da wata mata Mrs.Kafayat Adedoyin , Wakil yace har yanzu labarin da suke samu game da save matar Jan yanzu abubuwan sai a hankali, yace duk da haka suna sa idanu

In ba a manta ba mun kawo maku rahoton wan nan matsalar tsaro, da Yan bindiga suke kai hari a unguwar Birshin Fulani, inda matasa suka harzuka, suka fito zanga zanga lumana don nuna fushinsu da cewa abun ya ishesu haka.

Harin kwanan nan da suka kai shine na dauke wata mata da yayan ta uku Mrs. Rukayya Odedoyin, wacce aka sace ta a gidan ta, inda suka kulle yaranta a dakin lokacin da suka dauke ta.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment