Za Mu Karbi Tubabbun Boko Haram Hannu Biyu-Biyu – Shehun Borno

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi a ranar Laraba ya ce ana ta kokarin ganin an kammala shirin mayar da tubabbun mayakan Boko Haram cikin jama’a don samar da zaman lafiya mai dorewa cikin al’umma.

An ruwaito cewar Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiyan ya yi maganar ne a wani taro na kamfen din wayar da kai wurin kokarin mayar da tubabbun mayakan cikin jihar Borno.

A cewar sa ta’addanci a jihar ya dauki lokaci mai tsawo kuma mutanen jihar a shirye suke da a hada kan su da su don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cewar sa, tubabbun mayakan sun gane kuskuren su kuma a shirye suke da su cigaba da harkoki da jama’an gari. Kamar yadda ya ce: “Batun Boko Haram abu ne sananne a wurin mu kuma muna ta kokarin ganin kawo karshen wannan lamarin tsawon lokaci.

Da za a kawo karshen shi gaskiya da kowa ya ji dadi.” “Kamar yadda kowa ya sani, shugabannin gargajiya ciki har da dagacin kauyuka da malaman addini duk sun yarda da maganar mayar da su cikin jama’an gari.”

Shugaban ya roki jama’ar gari da su taru su yi aiki da shugabannin kananun hukumomi, gundumomi da shugabannin kauyaku wurin kawo zaman lafiya a jihar.

Anashi ?angaren Kwamishinan harkokin cikin gida, labarai da al’adu, Alhaji Babakura Abba Joto, ya ce yanzu haka mayakan da suka tuba sun kai 6,000 sai dai ba za a mayar dasu cikin jama’a ba har sai an gama tantance su an gyara su tukunna.

Kwamishinan harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, ta ce matan da suka mika wuya da dama sun shiga ta’addancin ne tun asali ba da son ran su ba.

Related posts

Leave a Comment