Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Barikin Sojoji

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu Tsagerun yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a ?aramar hukumar Sabon Gari, jihar Sokoto, inda suka kashe jami’ai da dama.

Wakilin Dailytrust ya gano cewa barikin sojojin dake a Kauyen Dama, an la?aba masa suna, “Sansanin Burkusuma.” Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai hari sansanin sojojin ne da sanyin safiyar ranar Jumu’a da ta gabata.

Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Idris Muhammad Gobir, ya shaidawa wani mutumi mai suna ?ancha?i, wanda ya tabbatar da kai harin.

Mutumin ya bayyana cewa maharan sun hallaka mutane da dama, sannan kuma an nemi wasu jami’an soji an rasa bayan harin. Bugu da ?ari tsagerun sun ?one motoci guda biyu, sannan suka yi awon gaba da wata guda ?aya, wacce suka yi amfani da ita wajen jigilar kayan abinci da suka sace a ?auyen.

Wani sanannen basarake a yankin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa an tura motoci barikin domin ?akko gawarwakin dakarun dojin da suka mutu a harin. Basaraken yace “Motocin sojoji sama da 10 sun bazama cikin jeji domin nemo maharan da kuma ?aukar fansa kansu.”

Wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya tabbatarwa wakilim Dailytrust cewa akwai jami’an hukumarsu uku da harin ya ritsa da su.

Related posts

Leave a Comment