Kaduna: An Yi Nasarar Damke Maharan Makarantar Bethel Baptist

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane uku da ke da hannu a sace dalibai sama da 100 na makarantar Bethel Baptist, dake Jihar Kaduna.

An rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba ne ya gabatar da wadanda ake zargin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, a hedikwatar runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS), a Abuja.

An tattaro cewa wadanda ake zargin, Adamu Bello, Isiaku Lawal da Muazu Abubakar, sun shaidawa manema labarai cewa su 25 ne suka sace daliban.

Sun bayyana cewar sun gudanar da aikin ne cikin tsananin neman kudi. “Mu ashirin da biyar ne muka gudanar da aikin. Mun yi garkuwa da dalibai 136 kuma mun samu sakon N100,000 daga kudin.”

Related posts

Leave a Comment