Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kwastam ta yi barazanar ?wace wasu jirage na ?ai?aikun jama’a 29 wa?anda masu su ba su biya kudaden fito ba.
A wani rahoto da ta fitar kakakin hukumar Joseph Attah, ya ce idan ba su bayyana kansu domin biyan ku?a?en da ake bin su to za a ?wace jiragen cikin kwanaki 14.
A ranar 31 ga watan Mayu kwastam ta sanar da shirinta na soma bincikar irin wadannan jirage a ?asar.
An gudanar da binciken ne tsakanin 7 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Agusta.
Attah ya ce a lokacin binciken mamalakan irin wadannan jirage mutum 86 sun hallara da gabatar da takardun da ake bukata.
Ya ce cikin 57 wadanda ake kasuwanci da su ne, sannan 29 ba su cika ka’idoji ba.
