?ungiyar SERAP mai fafutukar ya?i da cin hanci a Najeriya ta sake kai ?arar shugaba Buhari inda ta nemi kotu ta tilasta masabincikar zargin “bacewar sama da naira biliyan 881 a ma’aikatun gwamnati da hukumomi 367.”
SERAP ta ce ta shigar da ?arar ne a babbar kotun Abuja kuma ta nemi a gano ku?a?en da suka salwanta tare da hukunta wa?anda aka samu da laifin salwantarsu.
Ta ce gano ku?a?en zai taimakawa gwamnati maimakon kar?o rance.
SERAP ta ce ta shigar da ?arar ne bayan zarge-zargen da ke kunshe a cikin kashi na biyu na rahoton 2018 na babban akawun Najeriya da ya nuna cewa ma’aikatun gwamnati sun kashe sama da biliyan 880 ba tare da amincewa ba.
SERAP ta sha kai gwamnatin Najeriya ?ara kan batutuwa da dama amma har yanzu babu shari’a ?aya da aka yanke.
