Shari’ar Buhari Da Gwamnoni: Dole Gwamnoni Su Biya ‘Yan Kwangila – Malami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa Gwamnoni 36 na Najeriya cewa al?alami ya bushe, tilas sai sun biya ‘yan kwangila dala miliyan 418 ?in da hukuncin kotu ya gindaya masu.

Malami ya ce saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta fasa fara cire dala miliyan 418 a hankali ba ta na dannawa asusun ‘yan kwangilar domin Kotu ce ta yanke hukuncin cewa a biya su ku?a?en.

Kakkausan kalaman Malami sun zo ne mako ?aya bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta tsaida fara cirar ku?in daga asusun gwamnoni a ri?a biyan ‘yan kwangilar.

Su dai wa?annan ‘yan kwangilar sun kai gwamnonin jihohi 36 ?ara, inda su ka nemi a biya su ku?a?en aikin tuntu?a da su ka ce sun yi wa gwamnonin jihar, tsakanin 1995 da shekarun 2000, su ka taimaka domin a maida wa jihohin ku?a?en biyan bashin Paris Club da aka ri?a ?ibar masu fiye da ?a’ida.

Sun kuma yi i?irarin cewa sun yi aikin kwangiloli a jihohi 774 tun a wancan lokacin, amma ba a biya su ba.

Yayin da gwamnoni ke tababar ayyukan ‘yan kwangilar, su ma shugabannin ?ananan hukumomin Najeriya sun ce ba su ga wani aikin da ‘yan kwangilar su ka ce sun yi ba.

A ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ?ananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan ‘yan kwangilar masu i?irarin cewa sun yi wa jihohi da ?ananan hukumomi ayyukan adadin ku?a?en a shekarun baya.

Dillalan ‘yan kwangilar sun ce sun yi wa jihohi da ?ananan hukumomi aikin tuntu?a ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ?o?arin aikin dawo masu da ku?a?en da aka ri?a ?ibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.

Babban Mai Shari’a Iyang Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar ku?a?en da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.

Gwamnonin 36 sun shigar da ?arar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, wa?anda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).

A ?arar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa wa?ancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ?ananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.

Lauyoyin sun ce masu i?irarin sai an biya su ha??in ku?a?en har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.

“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi ku?a?e a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”

Daga cikin wa?anda gwamnoni 36 su ka kai ?ara, har da Ma’aikatar Harkokin Ku?a?e ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Ku?a?en Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Ku?a?en Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.

Related posts

Leave a Comment