Kwamitin Ha?akar Sanatoci da Majalisar Tarayya masu lura da Sufurin Jiragen Ruwa da Jiragen ?asa, sun ragargaji Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, dangane da abin da suka kira fifita Jamhuriyar Nijar a kan wasu sassan Najeriya.
Amaechi ya sha ragargazar ce a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamiti domin kare kasafin 2022 na ma’aikatar sa.
Tun da farko dai an fara tankiya ce a kan dalilin da ya sa za a gina titin Jibiya zuwa Mara?i na zamani, alhali kuma wanda za a gina daga Fatakwal zuwa Maiduguri ba na zamani ba.
Wato daga Jibiya zuwa Mara?i za a gina ‘Standard Gauge’, amma daga Fatakwal zuwa Maiduguri kuma za a gina ‘Narrow Gauge’.
Shugaban Kwamitin Sufuri na Majalisar Tarayya, Pat Asada ne ya fara ragargazar Minista Amaechi, inda ya bayyana cewa akwai rashin bada muhimmanci ga wasu ?angarorin ?asar nan a ?o?arin Amaechi na da?a?a wa al’ummar Jamhuriyar Nijar.
“Don me za ka yi ta giringi?ishin neman bashin gina titin jirgi mai nisan kilomita 284 daga Kano zuwa Nijar, alhali kuma ga wasu sassan ?asar nan, su na bu?atar titinan?
“Ka dubi irin harkokin kasuwancin da ake yi a yankin Kudu maso Gabas, ai su ne su ka fi bu?atar jiragen ?asa ba Mara?i ba.
“Mara?i ba ta kai muhimmancin Kudu maso Gabas ga tattalin arzikin ?asar nan ba. Ballantana kuma yankin Kudu maso Kudu.”
Shi kuma Sanata ?anjuma Goje, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sufurin Jiragen Ruwa, ya yi ?orafin cewa, “a gaskiya ku?a?en da ake kashewa wajen aikin titin jirgi daga Lagos zuwa Ibadan, sun yi yawa, kuma sun wace hankalin mai tunani.
Sannan kuma Goje ya tambayi Amaechi cewa, “shin laifin me muka yi maka a Kudu maso Gabas, Benuwai, Filato, Taraba, Bauchi, Gombe, Barno da Adamawa da ba za a yi mana titinan jirgin ?asa ba? Ko mu ba ‘yan Najeriya ba ne?”
Da ya ke maida jawabi, Amaechi ya ce ai babu wani bambanci tsakanin titunan jiragen. Na Mara?i da aka ce ‘standard gauge’ ne, ai iyakar tsawon wannan titin kilomita 20 ne kacal daga Jibiya zuwa Mara?i.
Babu Ku?in Aikin Titin Jirgin Kasa Da Ibadan Zuwa Kano -Amaechi:
Minista Amaechi ya ta?o batun ?arancin ku?a?e, ya shaida masu cewa yanzu haka babu ku?in da za a yi aikin titin jirgin ?asa daga Ibadan zuwa Kano.
“Saboda babu ku?in da za a yi aikin, sai an ciwo bashi. Saboda babu ku?in shi ya sa gwamantin tarayya ta ta?ar?ara za ta gina daga Kano zuwa Ibadan da kudin ta, kafin a samu bashin.”
Ya ?ara da cewa shi ma aikin gina titin Fatakwal zuwa Maiduguri duk babu ko sisi a ?asa, sai an ciwo bashi za a yi aikin tukunna.
