Za A Rage Yawan Fursunoni A Gidajen Yari – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce tana son ?ara rage yawan fursunonin da ke cikin gidajen gyara hali da ke fa?in ?asar domin rage cunkoso.

Mai bai wa Ministan harkokin cikin gida shawara kan harkokin watsa labarai Sola Faure ne ya tabbatar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ministan wato Rauf Aregbesola ya aika takarda ga gwamnonin ?asar domin neman ha?in kansu.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya bayyana cewa yana so ya tattauna da gwamonin ?asar domin sakin a?alla kashi talatin cikin ?ari na fursunonin da ke gidajen gyaran hali a fadin ?asar.

Ya bayyana cewa akwai bu?atar yin hakan sakamakon kashi 90 cikin 100 na fursunonin ?asar an tsare su ne sakamakon sa?a dokokin jihohi inda ya ce akwai kimanin fursunoni 75,635 da ke zaman jiran shari’a.

Mista Aregbesola ya bayyana cewa jimillar wa?anda suka saba dokokin gwamnatin tarayya da ke tsare a gidajen gyaran hali ba su wuce kashi 10 cikin 100 ba inda ya ce sauran wa?anda ke tsare duk suna da ala?a ne da sa?a dokokin jihohi.

Related posts

Leave a Comment