Babu Rigar Nono Ta Zinari A Kayan Da Muka Kwace Hannun Diezani – EFCC

Shugaban hukumar ya?i da rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa ya musanta rahotannin da ke yawo cewa akwai rigar mama ta gwal a cikin kayan da hukumar ta ?wace daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya.

Ana zargin Diezani wadda ta fice daga Najeriya a 2015 da satar ku?in da suka kai dala biliyan biyu da rabi daga asusun gwamnatin ?asa a lokacin da take minista, kodayake ta musanta zargin.

A watan Mayu ne Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya fa?a wa Majalisar Wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ?awa da aka ?wace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.

A watan Oktoba gwamnatin tarayya ta lissafa wasu kadarorinta da ta ?wace wa?anda suka ha?a da gidaje a Banana Island da ke Ikoyi ta Jihar Legas.

Sai dai da ya bayyana a kafar talabijin ta TVC ranar Laraba, Abdulrasheed Bawa ya ce labarin rigar mama ta gwal da aka ce akwai ta a cikin kayan na ?anzon kurege ne.

“Babu wani abu mai kama da rigar mama ta gwal, maganar ‘yan kafafen sada zumunta ce,” in ji shi.

“Zan iya fa?a muku a kyauta saboda ni ne jagoran wannan binciken. Ban san da ita ba. Idan da akwai ta ya kamata a ce na sani. Ya kamata na sani saboda ni na jagoranci binciken da sauransu.”

Related posts

Leave a Comment