Gagarimar matsalar tsaron da ta dabaibaye Najeriya tare da dagula tattalin arzikin ?asar, kusan ita ce babban dalilin da ya sa ake yawan ciwo basussuka domin cike gi?in da ake samu a Kasafin Ku?a?e.
Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed ce ta bayyana haka.
A kasafin 2022 dai Najeriya na sa ran za ta samu ku?in shiga naira tiriliyan 10, yayin da ta kasafta kashe Naira miliyan tiriliyan 16.
Wannan ya na nufin an samu gi?i kenan har na Naira tiriliyan 6, wa?anda Najeriya ta ce za ta cike sauran tiriliyan 6 ?in.
Ko a kasafin 2021 sai da aka samu gi?i wawakeken gi?i na Naira tiriliyan 5.2.
Yayin da ake fama da wannan yawan ciwo bashi, a gefe ?aya kuma bashin sai ?ara yawa ya ke yi.
Yadda bashin ke ?ara yawa, haka ita matsalar tsaro ke ?ara muni a fa?in ?asar nan.
Premium Times Hausa ta buga labarin yadda Sanata Lawan ya damu da wawakeken gi?in da aka samu.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya nuna damuwar yadda ake ta samun wawakeken gi?i a kasafin Najeriya, musamman na 2022.
Ya yi wannan ?orafin a ranar Alhamis, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Kasafin 2023 a Majalisa.
An dai samu gi?in zunzurutun Naira tiriliyan 6.26, wa?anda Buhari ya ce duk bashi za a rakito domin a cike gi?in.
Lawan ya ce yawan gi?in akwai abin dubawa sosai a ciki, don haka Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya za su bi kasafin filla-filla domin a yi masa aski, sasabe da kwaskwarimar rage wasu ku?a?e, ta yadda Najeriya za ta yi kasafin da zai zama daidai ?arfin aljihun ta, da kuma daidai ?arfin wuyan da zai iya ?aukar bashin da za a ciwo.
“Babbar matsalar da ke addabar kasafin ku?i a Najeriya ita ce matsalar yadda za a kar?i haraji da kuma ta yadda harajin ke shiga aljihun gwamnati.
A lokacin gabatar da kasafin, Buhari ya yi magana kan masu nuna damuwa da yawan bashin da ake ciwowa.
“Duk mai tantamar bashin da mu ke ciwowa ya je kawar da shakku a kan mu.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashin da gwamnatin sa ke ciwowa bai kumbura cikin da zai rikita ?asar nan ba.
Ya ce ayyukan da ake yi da kudaden da ake ciwowa bashi a bayyane su ke, don haka duk mai tantama zai iya fita ya yi bincike ya gani da kan sa.
Buhari ya yi wannan kalami a gaban gamayyar Sanatoci da Mambobin Majalisar Dattawa, yayin da ya ke gabatar masu da kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39.
A cikin kasafin dai ya bayyana cewa Naira tiriliyan 4.11 za a kashe su wajen biyan albashi da sauran ha??in tafiyar da ma’aikatan gwamnati.
Sai kuma zunzurutun Naira tiriliyan 3.61 wa?anda za su tafi wajen biyan basussukan baya, wanda gwamnati ke yi a kowane ?arshen wata.
Buhari ya ce za a kashe Naira biliyan 579 wajen biyan ha??in ‘yan fansho da biyan garatuti.
Yayin da Buhari ke jawabi, ya yi bitar wasu muhimman ayyukan da gwamnatin sa ta yi a shekarar da ta gabata, sannan kuma ya jinjina wa kan sa bisa ?o?arin da ya yi na tsayuwar sama da minti 50 ya na jawabi wajen gabatar da kasafin 2020. Kuma ya ce a wannan ranar ma zai yi bajintar sake yin irin waccan tsayuwar.
