Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Daure Maina Shekaru 61

Wata Babbar Kotun Tarayya a babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin garanbawul a harkar fansho Abdulrasheed Maina hukuncin ?aurin shekara 61 a gidan yari amma zai yi zaman shekara takwas ne a gidan kason.

Mai shari’a Okon Abang ya yanke wa Maina wannan hukunci ne kan laifuka 12 da suka ha?a da cin hanci da kuma halasta ku?a?en haram bayan shigar da ?ararsa da hukumar da ke ya?i da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ?asa EFCC ta yi.

Za a fara lissafa zaman gidan yarin ne daga 25 ga watan Oktoban 2019, wato lokaci na farko da kotun ta aike da Maina gidan kason, bayan da bukatar da lauyoyinsa suka gabatar ta neman beli ta gaza gamsar da kotun.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar jim ka?an bayan yanke wa Maina hukuncin ?aurin, ta ce wannan lamari wata gagarumar nasara ce a gare ta.

Sanarwar mai sa hannun mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ta ce EFCC ta yi nasarar tabbatar da dukkan abubuwan da ake bu?ata da suke cikin tuhumar, tare da yanke masa hukunci kan laifuka na 2 da 3 da 6 da 7 da 9 da kuma na 10 na tuhume-tuhumen.

Kazalika kotun ta umarci Maina da kamfaninsa mai suna Common Input Property and Investment Limited da su mayar wa da gwamnatin tarayya da kusan naira biliyan 2.1 da aka gano a asusun ajiyarsu na banki tare da bayar da umarnin rufe kamfanin.

Da farko dai kotu ta samu Maina da ?oye ainihin wane ne shi tare da sanya jami’an wasu bankuna biyu na Fidelity da UBA da su bu?e masa asusun ajiya ba tare da bin ?a’ida ba, inda yayin amfani da bayanan wani daga cikin iyalansa ba tare da saninsu ba.

An saka naira miliyan 300 da miliyan 500 da biliyan 1.5 lakadan a cikin biyu daga cikin asusun ajiyar bankunan.

Kotun ta ce Maina ya saci ku?a?en ?an fansho fansho ne wa?anda da “yawansu sun mutu ba tare da cin moriyar wahalar da suka yi ta tara ku?a?en ba,” saboda ya gaza bayyana yadda ya samu ku?a?en.

Sannan kotun ta ce albashinsa da alawus-alawus ?insa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati ba su kai ya tara wa?annan ku?a?e da ya mallaka ba.

Kotun ta kuma kama Maina da laifin sayen wata kadara a Abuja wacce ya biya dala miliyan 1.4 lakadan ba tare da biyansu ta banki ba.

A ranar takwas ga watan Oktoba ne kotu ta ?age sauraron ?arar bayan da Mai Shari’a Abang ya ?i amincewa da bu?atar lauyan Maina ta neman a ba da lokaci ya tsara adireshinsa a rubuce, inda lauyan masu shigara da ?ara ya soki bu?atar.

Wata shaida Rouqayyah Ibrahim ta shaida wa kotun yadda Maina ya mallaki kadarori a birnin Dubai na ?asar Ha?a??iyar Daular Larabawa UAE da Amurka da kuma wata kadara da ku?inta ya kai dala miliyan biyu a unguwar Jabi a Abuja.

Shaidar ta bayyana cewa an ?wato wasu bayanai har da 32 da ke da ala?a da kadarorin da Maina da iyalansa suka mallaka a Dubai da Amurka.

Rouqayyah ta kuma ce: “Bincike ya nuna cewa wani kamfaninsa a Dubai Northrich, yana da fiye da motoci 50 da ake masa harkar sufuri da su, sannan yana da wani katafaren gida a wata hamsha?iyar unguwa a Dubai.

“Matarsa Laila ita ma ta mallaki wani kamfanin tsaftace gidaje mai suna Spotless and Flawless. Sannan mun samu takardun shaidar biyan ku?a?e a yayin binciken,” in ji ta.

Shaidar ta kuma bayyana cewa binciken ya tabbatar da cewa wani kamfanin na Maina Kangolo Dynamic, ba ya wata harkar kasuwanci amma sai ya bu?e wani asusun ajiya da sunansa bai fito a ciki ba duk da cewa shi yake da iko da dukkan ku?a?en da ake zubawa a ciki.

Ta sake shaida wa kotun cewa wani binciken ya nuna kamfanin Colster Logistics mallakin Maina na da asusun ajiya a bankin Fidelity wanda aka zuba masa fiye da dala 400,000 daga lokacin da aka fara binciken.

Sannan an ?wato naira miliyan 500 dasga asusun ajiyar kamfanin Kangolo Dynamic cikin shekarun da Maina ke jagorantar kwamitin yi wa fansho garanbawul.

A ranar 10 ga watan Disamban 2020 ne Abdulrasheed Maina ya fa?i a kotu, lamarfin da ya tursasa Mai Shari’a Abang ?aga ?arar har sai ranar 21 ga watan Disamban 2020.

Sannan akwai lokacin da ya tsere daga ?asar bayan ba da belinsa amma jami’an tsaro suka kama shi a jamhuriyar Nijar aka mayar da shi Najeriya don ci gaba da fuskantar shari’a.

Related posts

Leave a Comment