Daga Aliyu Ahmad WAIWAYE Wanene Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali? Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, shi ne kusan batun da ya fi kowanne jan hankalin ma’abota shafukan sada zumunta a Nijeriya a ranakun karshen mako. Laftanal Kanal Abu Ali yana cikin sojoji biyar da suka rasa rayukansu a daren Juma’a, yayin bata kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori a jihar Borno. Rundunar sojojin Nijeriyar ta sha…
Read MoreCategory: Al’ajabi
Al’ajabi
Ana Tsiya A Legas: Gaye Ya Dirka Wa Kannenshi Mata Uku Ciki
Wani matashi da aka sakaya sunansa mai shekaru 24 ya yiwa kannensa mata 3 ciki a jihar Legas. Uwar yaran ta bayyana cewar, mahaifin yaran baya zama a gari yayin da yake tafiya fatauci, daga bisani itama ta bude shago take kasuwanci. Matar ta bayyana cewar, suna barin yaran nasu hudu a gida, inda babba yake da shekaru 24 yayin da ‘yar autarsu take da shekaru 16, sai dai yayin da yaran ke zaune su kadai a gida suna kallon finafinan. Matar ta fadi cewar, yaran sun shaida mata a…
Read MoreWasanni: Salah Ya Cigaba Da Rike Kanbi A Liverpool
Mohamed Salah ya ci gaba da nuna bajintar sa a Liverpool bayan da ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Atletico Madrid da ci 3-2 wanda hakan ya bada damar samun rukunin B a gasar zakarun Turai. Atletico ta yi rashin nasarar da ‘yan wasa goma a fili, bayan da aka kori Antoine Griezman a mintuna na 52 sakamakon yadda ya daga kafa fiye da kima har zuwa fuskar dan wasan Liverpool Roberto Firmino, bayan kwallaye biyu da ya zura a ragar Liverpool. Sauran wasannin rukuni-rukuni na gasar…
Read More‘Yan Bindiga Ba Su Da Manufa Kamar Boko Haram Da IPOB – Mohammed
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa da Al’adu, Lai Mohammed ya ce yan bindiga da ke adabar yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa bata gari ne kawai, wa?anda ba su da wata manufa akan ta’addancin da suke yi. Lai Mohammed ya ce suna da banbanci da yan Boko Haram da yan kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra wato IPOB, domin suna da manufofi da tuta akan ta’addancin su. A cewarsa, ‘yan bindigan bata gari ne kawai amma ba su jayayya da ikon Nigeria a…
Read MoreKano: Kotu Ta Bada Umarnin Cigaba Da Tsare AbdulJabbar Har Karshen Wata
Fitaccen malamin addini musuluncin nan a Kano Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda sabbin lauyoyinsa ke kare shi a kotu kan bayyana shaidu da suka gabatarwa kotu. Abduljabbar ya bayyana hakan ne a yayin zaman kotun na yau Alhamis da ya gudana a babbar kotun musulunci da ke kofar Kudu a birnin Kano. A yayin zaman kotun karkshin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, alkalin ya fara ne da tambayar sabbin alkalan Abduljabbar tuhume-tuhume da suka bukaci daukaka ?ara. Umar Mohammd da ke jagorantar tawagar sabbin lauyoyin,…
Read MoreMasari Ya Kalubalanci Alkalai Da Yin Gaggawa Wajen Yanke Hukunci
Gwamna Bello Masari na Jihar Katsina ya nuna matu?ar damuwa dangane da yadda masu shari’a da kotuna ke sakin ‘yan bindiga, masu fya?e da sauran masu aikata muggan laifuka da sunan beli. Masari ya nuna wannan damuwar jim ka?an bayan ya rantsar da sabbin al?alan manyan kotuna guda uku na Jihar Katsina. Daga nan sai ya yi kira ga ?ungiyar Lauyoyi ta Najeriya cewa ta ja kunnen mambobin ta, su daina fakewa da ‘yancin ?an Adam su na ?aure wa muggan masu laifi gindi ana sakin su. “Mu na cikin…
Read MoreDa Dumi-Dumi: EFCC Ta Cafke Sanata Barau Jibrin
Sanatan da ke wakiltar mazabar Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya shiga hannu kan zargin halatta kudaden haram, almundahanar kasafin kudi da wadatar da iyalansa ba bisa ka’ida ba. Ana kuma zargin Sanatan da amfani da kamfanonin da aka yi wa rajista da sunayen ‘ya’yansa da mukarrabansa don aiwatar da ayyukan mazabu da dama, ba tare da la’akari da tsarin da ya dace ba. Wadannan zarge -zargen suna kunshe ne a cikin takardar koken da Hukumar Matasan Arewacin Najeriya, NYCN ta mika wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da…
Read MoreGwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kisan Mutum 34 A Kudancin Jihar
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar labarin kisan mutane talatin da hudu da yan bindiga sukayi a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ranar Lahadi. Mun kawo muku cewa wasu batagari sun kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna. Kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi ranar Litinin, 27 ga Satumba, 2021. A cewarsa, kawo yanzu mutum 34 aka tabbatar da an kashe yayinda Sojoji suka kashe wutar da aka cinnawa…
Read MoreZa Mu Kawo Fasahar 5G A Shekarar Badi – Pantami
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, yace za’a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2022. Ministan ya bayyana cewa fasahar ta 5G zata taimaka matu?a gaya wajen rage aikata manyan laifuka na lalata kayayyakin gwamnati da sauran ayyukan ashsha. Pantami ya fa?i haka ne a Maiduguri, ranar Alhamis, a wurin taron da ma’aikatar ya?a labarai ta shirya kan lalata kayan ?angaren sadarwa da wutar lantarki. Ministan, wanda daraktan fasaha na hukumar…
Read More‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari Gonar Obasanjo
Rahotanni daga birnin Abeakuta na Jihar Ogun na bayyana cewar wasu ?an bindiga ?auke da muggan makamai sun kai hari gonar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta Ota dake Jihar da sanyin safiyar ranar yau. Rahotanni sun bayyana cewar muggan ‘yan Bindigar sun sace wasu ma’aika a gonar tsohon shugaban dake garin Kobape da ke jihar Ogun. Rahotanni sun ce maharan sun faki mutanen ne, tare da budewa motarsu wuta, kana daga baya suka yi awon gaba da su. Ko da yake ba a bayyana sunayen mutanen ba, amma manyan…
Read MoreFadan Karshe Da ‘Yan Bindiga: Duk Rintsi Ba Zan Bar Zamfara Ba – Matawalle
Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Bello Matawalle, ya soke duk wata tafiya da zata fitar da shi cikin jihar, dai dai lokacin da aka tsananta hare-hare kan yan bindiga. Da yake zantawa da kafar watsa labarai ta DW Rediyo, gwamnan yace matakan da aka ?auka kan yan bindiga ya fara haifar da ?a mai ido. Wane sakamako aka fara samu bayan ?aukar matakai? Matawalle ya bayyana cewa ?arayi sun fara sako wa?anda suka sace don dole domin ba su iya ciyar da su saboda…
Read MoreBauchi: Gwamna Ya Gargadi Sabuwar Majalisar Zartarwa
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya gargadi Sabon Sakataren Gwamnati da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin da Sabbin kwamishinoni, da suka sha rantsuwar kama aiki, Kan su jajirce wajen taimakama al’ummar Jihar, da aiki tukuru don samun dorewar mulkin gwamnati mai chi a karo na biyu a shekarar 2023 mai zuwa. Gwamnan yayi wan nan jan kunnen ne jim kadan bayan sabbin kwamishino sun sha rantsuwa, Wanda Babban jojin jihar ta rantsar dasu su Hajiya Rabi Talatu Umar, a babban dakin taro na gidan gwamnatin Jihar, tare da rattaba hanu kan takardar…
Read MoreBabu Inda Na Yanke Jiki Na Fadi – Tsohon Ministan Lantarki
A zantawar da BBC Hausa ta yi da tsohon Ministan Lantarki Sale Mamman ta wayar tarho, ya bayyana yanayin da yake ciki a yanzu. Tsohon ministan ya ce dama yana fama da rashin lafiya tun a ?arshen makon da ya gabata. “Tun kafin a sanar da wannan mataki dama ba ni da lafiya, don ko ofis ban je ba tun farkon makon nan.” Tsohon ministan ya dama ya dade ba shi da isasshiyar lafiya don yana yawan zuwa ganin likita ma akai-akai. “To a jiya Laraba da yau Alhamis ma…
Read MoreSai Buhari Ya Kau Za A Ga Alherin Da Ya Shuka – Fadar Shugaban Kasa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ji tasirin aikin da ya tafka a Najeriya bayan ya bar ofis a zaben 2023. Shugaban ya fadi haka ne bayan kaddamar da sabuwar gudanarwar Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA). A takaitaccen biki da aka gudanar a fadar gwamnati, Abuja, Buhari ya umarci hukumar da ta kara saka hannun jari da ke tallafawa fadada tattalin arziki, saboda an yi hasashen farashin mai na duniya zai ragu zuwa kusan dala 40 a kowace ganga nan da shekarar 2030. Shugaban ya sake jaddada…
Read MoreKano: Ba Za Mu Amince Da Halasta Shan Tabar Wiwi Ba – Ganduje
Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Jihohin Nijeriya. Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano. A sanarwar da kakakin Hukumar NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani…
Read MoreKano: An Kama Daraktan Hausa Fim Da Matar Aure
Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar an kama wani daraktan fim da wata sabuwar bazawara ?anya sharaf ko idda bata gama ba. Tabdijam!!! Ita dai wannan wannan Mata ta samu matsala da mijinta har saki ya shiga, anyi ittifa?in cewa ko idda bata gama ba, inda ta ?auko ?afa tun daga garin Zazzau zuwa birnin Kano, ba don komai ba sai don ta soma harkar fina finan Hausa salon Kannywood. Ko da mahaifin yarinyar ya duba sama ko ?asa baiga wannan matashiyar-kuma-?anyar Mace tuni ya garzayo jihar Kano domin…
Read MoreGwamnatin Buhari Ta Gaza Wajen Samar Da Tsaro – ?ungiyar Kare Hakkin Bil-Adama
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana takaicin ta game da gazawar gwamnatin tarayyar Najeriya na samarwa jama’ar kasar tsaron da ya kamata. Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar, game da yanayin da tsaro ke ciki a Najeriyar. A cewar Amnesty International cikin wata guda kadai an kashe mutane 112 a rikice-rikicen da aka samu a jihohin Kaduna da Plateau a Najeriyar. Kungiyar cikin rahoton da ta fitar ta ce baya ga mutanen da suka hallaka dalilin rikice-rikicen, masu garkuwa da mutane…
Read MoreBauchi: Hukumar Tsaftar Muhalli Da JNI Sun Sha Alwashin Kawar Da Zaizayar Kasa
Hukumar kula da tsaftace muhalli ta Jihar Bauchi da Kungiyar Jama’atun-Nasurul-Islam reshen Jihar, sunsha al’washin kawar da matsalar zaizayar kasa da take addaban yankin arewa maso gabashin Najeriya ta hanyar dashen itatuwa, Hakan yana dauke ne a cikin jawabin Shugaban hukumar Dakta Ibrahim Kabir a lokacin da kwamitin Jama’tun nasarul Islam takai wata ziyara ta hadin gwiwa. Shugaban yace wan nan ziyara da kungiyar jama’atu ta kai, yazo a kan gaban da hukumar take da shirye-shirye na musamman kan dakile matsalar kwararuwar hamada da kuma barazanar zaizaiyar kasa a dukkan…
Read MoreBatanci Ga Buhari: APC Ta Dakatar Da Shugaban Jam’iyya A Adamawa
Jam iyar A P C a jahar Adamawa ta dakatar da shugabàn rikon jam iyar a karamar hukumar yola ta kudu Alh. Suleiman Adamu biyo bayan zarginsa da zagin shugaban kasa muhammadu Buhari. Kwamitin aiyukan jam iyar dake jahar ta Adamawa ne ya dauki matakin haka a taron gaggawa da sukayi dangane da lamarin a cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa. A wata sanarwa daga mai magana da yawun jam iyar na riko Muhammed Abdullahi na baiyana cewa an dauki matakin dakatar da shugabàn rikonne biyo bayan…
Read MoreZan Koya Wa Mataimakina Hankali – Matawalle
Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Jihar Bello Matawalle, a ranar Asabar ya ce ba zai yarda da halin rashin ladabi daga mataimakinsa, Mahdi Aliyu ba, ko ka?an domin ba sa’an shi bane. Matawalle ya fusata ne kan wani taron siyasa da aka yi kwanan nan wanda mataimakin gwamnan ya yi domin sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar hamayya ta PDP. Dukkansu sun shigo gwamnati ne a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar PDP amma Matawalle da kusan dukkanin zababbun shugabanni a jihar a watan da ya gabata,…
Read More