Kano: Ba Za Mu Amince Da Halasta Shan Tabar Wiwi Ba – Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Jihohin Nijeriya.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano.

A sanarwar da kakakin Hukumar NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani dan majalisar tarayya daga jiharsa da zai goyi bayan irin wannan yunkurin, gaba ?aya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa ziyarar na NDLEA zuwa Kano na cikin shirin yakin da hukumar ke yi na ta’amulli da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi.

Ganduje ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano bata goyon bayan sha a fataucin miyagun kwayoyi, addinin da ya fi wanzuwa a jihar na Islama shima ya hana sha da fataucin miyagun kwayoyi. Ya ce: “Kano ce jihar mafi yawan yan majalisu a majalisar tarayya. Ina son in tabbatar maka babu wanda zai goyi bayan hallasta ganyen wiwi a cikinsu. “Za kuma mu amince da bukatar ka na neman fili domin gina gidajen jami’an hukumar reshen jihar Kano.”

Tunda farko, Marwa ya bukaci gwamnan kada ya goyi bayan duk wani yunkuri na halasta amfani da ganyen wiwi da wasu zababbun yan majalisa ke yi. Ya ce a halin yanzu NDLEA na aiki tukuru don ganin ta takaita bazuwar haramtaciyar kwayar a Nigeria. Ya ce halasta haramtaciyar ganyen zai janyo koma baya ga nasarar da hukumar ta samu kawo yanzu.

Related posts

Leave a Comment