Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ji tasirin aikin da ya tafka a Najeriya bayan ya bar ofis a zaben 2023.
Shugaban ya fadi haka ne bayan kaddamar da sabuwar gudanarwar Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA).
A takaitaccen biki da aka gudanar a fadar gwamnati, Abuja, Buhari ya umarci hukumar da ta kara saka hannun jari da ke tallafawa fadada tattalin arziki, saboda an yi hasashen farashin mai na duniya zai ragu zuwa kusan dala 40 a kowace ganga nan da shekarar 2030.
Shugaban ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyuka na dogon lokaci da shirye-shiryen da ke samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.
