Kano: An Kama Daraktan Hausa Fim Da Matar Aure

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar an kama wani daraktan fim da wata sabuwar bazawara ?anya sharaf ko idda bata gama ba. Tabdijam!!!

Ita dai wannan wannan Mata ta samu matsala da mijinta har saki ya shiga, anyi ittifa?in cewa ko idda bata gama ba, inda ta ?auko ?afa tun daga garin Zazzau zuwa birnin Kano, ba don komai ba sai don ta soma harkar fina finan Hausa salon Kannywood.

Ko da mahaifin yarinyar ya duba sama ko ?asa baiga wannan matashiyar-kuma-?anyar Mace tuni ya garzayo jihar Kano domin ?o?arin ganin yayi ido hu?u da wannan ?iya tasa, data gudu daga gida ana tsaka da tsala ruwan sama.

Isar sa Kano keda wuya, ya bazama ka’in da na’in wajen neman ?iyar tasa, har ya kai ga isa ofishin hukumar Hisbah ta jihar Kano, inda ya dam?a masu hoton ta.

Nan da nan kuwa hukumar Hisbah tayi wani salon kai sumame, irin na ?warewa. Abin ku da ?wararru, tuni suka cimma nasarar cafke wannan ?anyar bazawara a hannun wani mai bada umarni a fim ?in Hausa, inda ta baje kolin ta a gidan wata jaruma dake masana’antar ta Kannywood.

Ita dai wannan bazawara ana zargin ta ha?a kai ne ita da mahaifiyar ta domin shigowa garin Kanon.

Da aka tambayi mahaifin yarinyar ko me yasa bayason harkar ta fim?

Mutumin ya kara da cewa:

“Bamason harkar ta fim ne saboda harka ce ta watsewa, harka ce ta lalata. Duk uba nagari ko uwa ta gari ba zasu so ?a?ansu su shiga wannan shiri ba”.

Da aka tambayesa, cewar, ai su ?an fim ?in nacewa sana’a suke yi, dattijon ya ?ara da cewa:

“Mace lokaci ne da ita, idan ?a namiji ne yaje yayi ta yi, amma ba mace ba. Aure yafi fim, daga duniya har lahira”.

Daga ?arshe dattijon yayiwa ?iyar tasa addu’a, akan Allah ya shirya ta shirin addini.

Daga Jaridar Mikiya

Related posts

Leave a Comment