Jam iyar A P C a jahar Adamawa ta dakatar da shugabàn rikon jam iyar a karamar hukumar yola ta kudu Alh. Suleiman Adamu biyo bayan zarginsa da zagin shugaban kasa muhammadu Buhari.
Kwamitin aiyukan jam iyar dake jahar ta Adamawa ne ya dauki matakin haka a taron gaggawa da sukayi dangane da lamarin a cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa.
A wata sanarwa daga mai magana da yawun jam iyar na riko Muhammed Abdullahi na baiyana cewa an dauki matakin dakatar da shugabàn rikonne biyo bayan zarginsa da zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani mryar da aka nada kuma ya ta yawo a kafafen sada zumunta.
An dai jiyo Suleiman Adamu na cewa dama korona ta hallak shugaba Buhari kuma mataimakinsa Yemi Osinbajo ya maye gurbinsa.
Tunin dai kwamitin ya kafa kwamiti mai mutum bakwai da zai gudanar da bincike domin gano sahihin lamarin domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Kuma tunin mataimakin shugaban da aka dakatar din wato Alhaji Adamu Majekano ya maye gurbinsa a matsayin shugaban rikon Jam iyar a karamar hukumar yola ta kudu dake jahar Adamawa.
Cikin wadanda suka halarci tarondai sun hada da tsohon gwamnan jahar Adamawa Jibrilla Bindow da tsohon kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Kabiru Mijinyawa da dai sauransu.
Kwamitin ladabtarwan dai sun hada da Alh, Saidu Naira a matsayin shugaba sai Barista Shagnah Pwamaddi a matsayin sakatare sai kuma Abdullahi Wali da sauransu a matsayin membobi.
Jàm iyar ta kuma kirayi membobinta da su kaucewa duk abunda zai kawo rarrabuwan kan Jam iyar bak daya.
