Bauchi: Hukumar Tsaftar Muhalli Da JNI Sun Sha Alwashin Kawar Da Zaizayar Kasa

Hukumar kula da tsaftace muhalli ta Jihar Bauchi da Kungiyar Jama’atun-Nasurul-Islam reshen Jihar, sunsha al’washin kawar da matsalar zaizayar kasa da take addaban yankin arewa maso gabashin Najeriya ta hanyar dashen itatuwa,

Hakan yana dauke ne a cikin jawabin Shugaban hukumar Dakta Ibrahim Kabir a lokacin da kwamitin Jama’tun nasarul Islam takai wata ziyara ta hadin gwiwa.

Shugaban yace wan nan ziyara da kungiyar jama’atu ta kai, yazo a kan gaban da hukumar take da shirye-shirye na musamman kan dakile matsalar kwararuwar hamada da kuma barazanar zaizaiyar kasa a dukkan kananan hukumomi ashirin na Jihar.

Kana ya kara da cewa muhimmanci dashen itatuwa na da matukar alfanu ga rayuwar Dan-Adam in akayi la’akari da iskar numfashi da mutane suke shaka da Kuma gyaran yanayi na muhalli, da kawata wurare da kuma uwa uba Kare kasa daga zaizayewa,

Dakta Ibrahim, yayi nuni da cewa in aka samu hadin Kai daga al’umma to za Adamu cin nasara a hidimar kula da muhalli da tsafatce wuraren da Jama’a suke harkokinsu nanyau da kullun, don inganta kiwon lafiya, da kuma rage cututtuka da ake shakar su ta hanyar shakan iska baki daya.

Ana su Kwamitin da Hakimin Gamawa Adamu Abdulkadir Dahuwa ya jagoranta karkashin Kungiyar Jama’atun, nasarul Islam, jim kadan bayan sun kammala ganawa a hukumance, yace sun zo ne a matsayin su na kwamitin kula da hidimar shuken-ahuken itatuwa don kaucewa barazanar kwararowar hamada da zaizayar kasa, a cewarsa Jihar Bauchi tana daya daga cikin jihohin da suke fuskanta wan nan babban matsala.

Hakimin yace, “maganan dashen itatuwa kuwa abune da zai inganta muhalli, da ci gaban al’umma, shiyasa Kungiyar jama’atu ta yunkura don Kawar da wan nan matsalar tare da hadin gwiwa da hukumar BASEPA da Kuma ganin ta wace hanya zamu samu ta hadaka, domin samar da dashen itatuwa da kuma samun shawarwari na musamman Kan wan nan batu”.

Kana daga karshe hukumar tare da kungiyar sunyi kira ga al’umma da suroka bada hadin kai don ganin an cimma burin gwamnati ta Hanya shuke- shuke itatuwan a wurare da dama don tsaftace wa tare da inganta muhallin.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment