Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya gargadi Sabon Sakataren Gwamnati da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin da Sabbin kwamishinoni, da suka sha rantsuwar kama aiki, Kan su jajirce wajen taimakama al’ummar Jihar, da aiki tukuru don samun dorewar mulkin gwamnati mai chi a karo na biyu a shekarar 2023 mai zuwa.
Gwamnan yayi wan nan jan kunnen ne jim kadan bayan sabbin kwamishino sun sha rantsuwa, Wanda Babban jojin jihar ta rantsar dasu su Hajiya Rabi Talatu Umar, a babban dakin taro na gidan gwamnatin Jihar, tare da rattaba hanu kan takardar kama aiki gadan gadan.
Indai ba a manta ba kimanin watanin uku kenan gwamnatin jihar take gudanar da mulki ba tare da Yan’majalisan zartarwar ba, biyo bayan sauke su a wanchan lokaci da Gwamnan yayi da cewa yayi hakan ne don sake Shan dammara tun karar kalubale irin na siyasa, a yanzu haka Sabon zubin da gwamnan yayi kosan dukkan su sun sake dawowa in banda yan’kalilan a cikinsu.
Kana Gwamnan ya Kara da cewa nan gaba kadan lokacin da za’a fada cikin hidimar siyasa gadan gadan zai kan Kama, ya Kuma gargade su da Kar su yarda subfada ciki hidimar cinnhanchi darashawa domin a cewarsa gwamnatin sa tazo ne, ba don komai ba sai don suyi ma al’ummar Jihar aiki babu kama hannun yaro.
Gwamna Bala ya nanta cewa, “dole ne ku zama masu gaskiya da rokon Amana, muna sa ran zaku zama wakilai Jama’ar ku masu adalchi tare da rike kowa ba tare da nuna banbance ba, Kuma ku nuna masu yadda aikin mu take wakana a gwamnatance karku zo kunbamu Kunya, bayan mun sake baku dama ko Kuma amana a karo na biyu!”.
Yace mun dauki lokaci mai tsawo tare da yin nazari don muga munyi abunda al’umma zasu fita a cikin ukuba, da matsatsin rayuwa, ba akoma baya ana cin kafafun mu ba, “Shekarar 2023 tana karatuwa, muna da bukatar toshe duk wata baraka daka iya kawo mana turniki ko cikas a tafiyarmu na sake mulkin jihar a karo na biyu, domin muciyar da Jihar mu gaba”
Bala yace chin zabe ya ta’allaka ne da samun goyon bayan jama’ar gari, hakan nan ya Kara tabbatar masu da cewa dole sai sun hada Kai da yannmajalisar dokoki na Jihar domin gudanar da aikinsu, duk da ba jam’iyyarsu ce Mai rin Jaye a Jihar ba, amma saboda sun da Al’umman Bauchi ne a gaba shiyasa suke gudanar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali tsakaninsu da yayan jamiyyar Adawa ta APC musamman yan’majalisun dokokin jihar.
Wadanda gwamnan ya rantsar dai Sunsha alwashinbaima ma.ra da kunya suna Mai tabbatar ma da gwamnan bada tasu gudumuwar wajenngina al’umma da mutunta kowa don ci gaban Jihar Bauchi baki daya, inda yawancin kwamishinonin sun koma maikatunsu da suka bari a baya.
Daga Adamu Shehu Bauchi
